Nigerian news All categories All tags
Ganawar Buhari da gwamnonin APC: Hotuna da rahoton abinda ya faru

Ganawar Buhari da gwamnonin APC: Hotuna da rahoton abinda ya faru

Rahotanni da jaridar Legit.ng ta samu sun tabbatar da cewar an kasa cimma daidaito yayin ganawar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gwamnonin jam’iyyar APC da aka yi a yau, Talata, a fadar gwamnatin tarayya.

An fara taron ne da misalign karfe 2:15 na rana sannan an kare da misalign 3:30, dukkan gwamnonin da sun ki yin magana da manema labarai dake dako a fadar gwamnati domin jin yadda ganawar su ta kasance.

Gwamnonin jihohin Kebbi da na Filato, Atiku Bagudu da Simon Lalong, ne suka bayar da addu’o’in bude taron.

Ganawar Buhari da gwamnonin APC: Hotuna da rahoton abinda ya faru

Ganawar Buhari da gwamnonin APC

Wani bincike ya tabbatar da cewar karin wa’adin shugabannin jamiyyar APC ne makasudin taron da kuma batun yin shugabancin rikon kwaryar jam’iyyar karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole.

Mafi yawa daga cikin gwamnonin jam’iyyar na goyon bayan Karin wa’adi ga shugaban jam’iyyar, John Oyegun.

Ganawar Buhari da gwamnonin APC: Hotuna da rahoton abinda ya faru

Gwamnonin APC

Dukkan gwamnonin da manema labarai suka tunkara, da suka hada da Rochas Okorocha, Nasir El-Rufa’I, da Simon Lalong sun ce sun cimma yarjejeniyar cewar babu wanda zai yi magana a kan abinda aka tattauna yayin ganawar ta su.

DUBA WANNAN: Dumu-dumu: An kama wasu matasa suna sata a wani gida a Kano, duba hotunansu

Rahotanni sun bayyana cewar shugaba Buhari ya bukaci gwamnonin da su saka wata ranar domin cigaba da tattauna a kan batutuwan shugabancin jam’iyyar. Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz yari, ya zabi ranakun 9 da 10 ga watan Afrilun da muke ciki domin cigaba da taron. Saidai gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’I ya kalubalance shi a kan dalilinsa na saka ranakun 9 da 10 ga watan.

Ganawar Buhari da gwamnonin APC: Hotuna da rahoton abinda ya faru

Wasu gwamnonin APC

Rahotanni sun bayyana cewar gwamnonin sun gaza cimma matsaya, daga karshe haka suka watse wasu daga cikinsu cikin fushi yayin da wasu suka yi ta maza tare da yin murmushi ga manema labarai.

Saidai anji muryar wani gwamna yayin da yake magana da takwaransa, yana fadin “ba wani mutum da ya isa ya mayar da mu rakumi da akala, ba zata yiwu ba.

Ganawar Buhari da gwamnonin APC: Hotuna da rahoton abinda ya faru

Gwamnonin APC

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel