Nigerian news All categories All tags
Noma ya hanani kashe kaina saboda rashin aikin yi – Inji wata matashiya

Noma ya hanani kashe kaina saboda rashin aikin yi – Inji wata matashiya

- Miss Felicia Ezekiel, matashiyace data gama jami’a amma ba aikinyi, tace shigarta harkar noma ya hanata kashe kanta

- Ezekiel tsohuwar daliba ce a jami’ar birnin tarayya wadda take da Digiri a fannanin lissafin kudi

- Ta tina cewa shigarta harkar noma ta hana mugun tinanin da takeyi na kashe kanta saboda damuwa na zaman gida

Miss Felicia Ezekiel, matashiya ce data gama jami’a amma ba aikinyi, tace shigarta harkar noma ya hanata kashe kanta.

Ezekiel tsohuwar daliba ce a jami’ar birnin tarayya wadda take da Digiri a fannanin lissafin kudi.

Ta tina cewa shigarta harkar noma ta hana mugun tinanin da takeyi na kashe kanta saboda damuwa na zaman gida shekara uku bayan gama makaranta ba aikinyi. “Tace na fara ne da aron gona akan N20,000 a shekara, a Kugbaru dake karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa”.

Noma ya hanani kashe kaina saboda rashin aikin yi – Inji wata matashiya

Noma ya hanani kashe kaina saboda rashin aikin yi – Inji wata matashiya

Ezekiel tace, noman ganyen Ugwu ya magance mata duk wata matsala dake damunta, saboda yanzu tana cikin farin ciki sakamakon abunda take samu daga wannan noma da takeyi.

KU KARANTA KUMA: Wakilan Jihar Kaduna basu amince da Majalisa ba akan batun hana ciwo bashi

“ina da ‘yan uwa biyu da suka gama makaranta ba aikinyi da mahaifiyata da bata aiki, da kanne. Amma ta wannan hanyar ta noman Ugwu dashi nake biyan kudin haya, in biyawa kannena kudin makaranta, kai karshe ma har gida nake ginawa”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel