Nigerian news All categories All tags
Wakilan Jihar Kaduna basu amince da Majalisa ba akan batun hana ciwo bashi

Wakilan Jihar Kaduna basu amince da Majalisa ba akan batun hana ciwo bashi

- Mambobi 15 na majalisar wakilai a jihar Kaduna sunyi korafi bisaga kin yadda da bayar da bashi na bankin duniya na $350

- Wasu cikin mambobin na PDP da APC sun goyi bayan gwamnatin jihar a kan kokarin neman bashin don hakan zai kawo cigaba a jihar

- Mambobin suna ganin cewa kiyawar da ‘yan majalisar sukayi son rai ne na siyasa wadanda ya kamata ace sun fifita bukatar jama’a akan son ransu

Mambobi 15 na majalisar wakilai a jihar Kaduna sunyi korafi bisaga kin yadda da bayar da bashi na bankin duniya na $350. Wasu cikin mambobin na PDP da APC sun goyi bayan gwamnatin jihar a kan kokarin neman bashin don hakan zai kawo cigaba a jihar.

Mambobin suna ganin cewa kiyawar da ‘yan majalisar sukayi son rai ne na siyasa wadanda ya kamata ace sun fifita bukatar jama’a akan son ransu. Amma Ciyaman na kwamitin kula da basussuka na gida da waje na Sanatocin, Shehu Sani yace, ba wani batanci da zaisa shi da sauran mambobi su yadda da neman wannan bashi.

A shekarar 2017, Gwamnatin jihar Kaduna ta nemi bashi bashi ta hanyar gwamnatin tarayyan da ta bata izini akan ta karbi bashin kudi do gudanar da ayyukan cigaba a na bangaren kiwon lafiya da inganta ilimi a jihar.

A ranar Alhamis 29 ga watan Maris, majalisar taki amincewa da karbar bashin bayan Sanatoci uku daga jihar sun nuna rashin goyon baya ga lamarin.

KU KARANTA KUMA: Buhari na samun rinjaye a majalisa kan rigimar da sukeyi da majalisar

Gwamnatin jihar kuma tace duk wata ka’ida da karbar bashin sun cika ta shiyasa ma har bankin ya amince da bayar da bashin.

Masu fada a ji na jihar sunce ra’ayin al’umma na jihar nag aba da ra’ayi Sanatoci uku, wadanda suka nuna rashin amincewarsu ga karbar bashin, shiyasa suke rokon Sanatocin dasu cire son zuciya a cikin lamuransu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel