Nigerian news All categories All tags
Gwamnan jihar Kogi ya fado ba daidai ba daga motarsa, ya turgude kafa

Gwamnan jihar Kogi ya fado ba daidai ba daga motarsa, ya turgude kafa

Wani ibtila’I ya fada ma Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a gidan gwamnatin jihar dake garin Lokoja, inda ya samu targade bayan ya diro ba daidai ba daga motarsa, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Babban daraktan watsa labaru na fadar gwamnatin jihar, Kingsley Fanwo ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata 3 ga watan Maris, inda yake musanta wasu rahoto dake cewa gwamnan ya gamu da mummunan ciwo har ma baya iya motsi.

KU KARANTA: Matsalar shaye shaye a tsakanin matasan Arewa: Kulalliyar shiri ne na Inyamurai – Inji wani Malami

Fanwo yace a ranar Juma’a 31 ga watan Maris ne Gwamna Yahaya Bello a garin sauka daga mota ya fado ba daidai ba, inda ya samu targade a kafarsa ta hagu, bayan nan likitoci sun duba shi, suka daure kafar, daga nan suka sallame shi.

Gwamnan jihar Kogi ya fado ba daidai ba daga motarsa, ya turgude kafa

Gwamnan jihar Kogi

Daga karshe sanarwar ta gode ma masoya gwamnan da suka yi tuntuba don jin gaskiyar halin da gwamnan ke ciki, tare da aikawa da sakon gwamnan na taya murnar bikin Easter ga jama’an jihar Kogi gaba daya.

Da fari dai an samu wasu rahotanni masu tayar da hankula dake cewa wai gwamnan ya gamu da wata mummunan ibtila’I da tayi sanadiyyar kwantar da shi a Asibiti, inda wasu kuma ce yada jita jitan cewa baya iya motsi ma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel