Nigerian news All categories All tags
Da lauje cikin naɗi: Batun sauyin lokutan zaɓe

Da lauje cikin naɗi: Batun sauyin lokutan zaɓe

- Ya kamata a daina yi wa dokoki karantsaye

- Kowacce hukuma na da yadda doka ta faɗi yadda zata gudanar da aikinta

An bayyana yuƙurin da majalisar ƙasar nan take na kwaskwarimar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) zata gudanar da zaɓuka a kasar nan gabannin babban zaɓen 2019 da cewa, yi wa doka karan tsaye ne.

Sauya jadawalin zabe

Sauya jadawalin zabe

Da yake bayyana hakan a wata tattaunawarsa da ƴan Jaridu, tsohon babban kwamishinan Shari'a na Jihar Bauchi Ibrahim Umar ya ce, tabbas ba dai-dai ba ne yunkurin da majalisar take na sauya yadda za'a gudanar da zaɓen 2019.

Umar ya faɗi hakan ne, bayan da ya jaddada aniyarsa ta tsayawa takarar majalisar wakilai.

KU KARANTA: Jerin Yaruka 17 mafi shahara a fadin duniya

A cewarsa, yunkurin tamkar katsalandan ne ga aikin hukumar zaɓen ta ƙasa (INEC).

"INEC ce kaɗai ke da haƙƙin sauya yadda za'a gudanar da zaɓe kamar yadda dokar da ta kafa hukumar ta tanadar."

Ya ci gaba da cewa,

"A matsayinta na hukuma mai cikakken ƴanci, ita take da ikon canja yadda zata gudanar da aiyukanta ba tare da anyi mata wani kutse ko shisshigi ba, a saboda haka ya zama wajibi a ƙyalesu su gudanar da aikinsu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel