2019: Gwamnonin APC zasu gana da shugaba Buhari a yau

2019: Gwamnonin APC zasu gana da shugaba Buhari a yau

- Gwamnonin APC zasu sake ganawa da shugaba Buhari

- Ana sanya ran zasu sake masa batun sake takara a 2019

- Za kuma su tattauna kan wasu muhimman batutuiwa da suka shafi kasar dama jam'iyyar

Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zasu gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarinsu na ganin ya sake takara a 2019.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta tattaro cewa ganawar wanda aka shiya yi da misalin karfe 2 na rana, zai kunshi tattaunawa kan wasu matsaloli na kasar dama jam’iyyar ciki harda kin amincewa da tsawaita wa’adin shugabannin APC.

2019: Gwamnonin APC zasu gana da shugaba Buhari a yau

2019: Gwamnonin APC zasu gana da shugaba Buhari a yau

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP tayi babban asara a jihar Yobe inda mambobinta 7000 suka koma jam’iyyar APC

A kwanakin baya ne dai majalisar koli ta jam’iyyar APC ta dauki matakin kara ma shuwagabannin jam’iyyar APC wa’adin mulki na tsawon shekara guda daya, tun daga mazabu har zuwa matakin kasa gaba daya, sai dai matakin bai dace tsarin mulkin jam’iyyar ba, inji Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel