Komai nisan jifa: An kama dukkan 'yan dabar Dino Melaye da suka tsere daga hannun 'yan sanda, ku kalli fuskokinsu

Komai nisan jifa: An kama dukkan 'yan dabar Dino Melaye da suka tsere daga hannun 'yan sanda, ku kalli fuskokinsu

- Yan sanda sun sake kamo dukkan wandanda ake nema ruwa a jallo bayan sun tsere daga hannun yan sanda a jihar Kogi

- Ana tuhumar su ne da yiwa Sanata Dino Melaye aiki a matsayin yan bangan siyasa da ma aikata kisa

- Rahotanni sun ce biyu daga cikin shida da ake tuhuma sun amsa cewa Dino Melaye ne ke daukan nauyin su

Hukumar Yan sandan Najeriya ta sake kamo dukkan mutane shida da aka bayar da sanarwan neman su ruwa a jallo bayan sun tsere daga hannun Yan sanda a ranar 28 ga watan Maris daga jihar Kogi.

Rahotanni daga shafin Twitter na Hukumar Yan sanda ya nuna cewa Kabiru Seidu (Osama), Nuhu Salisu (Small), Aliyu Isa, Adams Suleiman, Emmanuel Audu da Musa Mohammed wanda aka tsare a ofishin Yan sanda na A Division sun tsere ne a ranar da za'a gurfanar da su gaban kuliya a Lokoja babban birnin jihar Kogi.

Yanzu-Yanzu: An sake kamo yan dabar da sukayi ikirarin Dino Melaye ne ke daukan nauyin su

Yanzu-Yanzu: An sake kamo yan dabar da sukayi ikirarin Dino Melaye ne ke daukan nauyin su

Legit.ng ta gano cewa am tsare su da na farko bisa zargin suna yiwa Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye aiki a matsayin yan bangar siyasa da kuma aikata kisa.

Tuni dai Dino Melaye ya musanta batun inda ya ce shi sharri ake son yi masa har ma yayi barazanar kai Hukumar Yan sanda kara Kotu saboda bata masa suna.

Yanzu-Yanzu: An sake kamo yan dabar da sukayi ikirarin Dino Melaye ne ke daukan nauyin su

Yanzu-Yanzu: An sake kamo yan dabar da sukayi ikirarin Dino Melaye ne ke daukan nauyin su

KU KARANTA: Wata mata ta watsawa mijinta ruwan zafi hade da yaji a kan danta

A rahotannin da This Day ta ruwaito, an kama wandanda ake zargin ne a wurare daban-daban, a makon da ya wuce an kama Seidu a ranar 1 ga watan Afrilu a jihar Bauchi. An ruwaito cewa an tsare Seidu ne a hedkwatan yan Sanda da ke Abuja.

Sanarwan da hukumar yan sandan ta bayar ya bayyana cewa an dage rannan da za'a gurfaranar da su gaban kotu zuwa 10 ga watan Mayun 2018.

Shugaban kungiyar yan ta'addan, Kabiru Seidu wanda akafi sani da Osama ya shaida wa yan sanda cewa ya kasance yana yiwa wani dan siyasa mai suna Alhaji Mohammed Audu aiki kuma shine ya kai shi Abuja inda ya hada shi da Sanata Dino Melaye a hanyar zuwa filin jirgin sama a ranar watan Disambar 2017.

A baya Saidu ya fadawa yan sanda cewa Dino Melaye ya bashi jakka dauke da bindigar kirar AK47 guda daya, wasu kananan bindigogin biyu da kuma kudi N430,000.00 don ya raba tare da sauran yan kungiyar.

Yan sandan kuma sun kama wasu mutanen da aka samu su da hannu wajen taimakawa wadanda ake zargi wajen guduwa da kuma boyewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel