Nigerian news All categories All tags
Barayin gwamnati: Ku cire suna na daga ciki

Barayin gwamnati: Ku cire suna na daga ciki

- Hujja ya kamata ka samar ba magana a kafar yada labarai ba

- Har yanzu sun gaza nuna shaidar da zata tabbatar da zargin da suke min

Tsohuwar minista a gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan, kuma Sanata a mazabar arewa ta Jihar Anambra Uwargida Stella Oduah, ta ce har ya zuwa yanzu ba wata hujja da ta tabbatar da zargin cewa da hannun ta cikin badakalar Naira biliyan tara da dubu dari takwas.

A cewarta, wannan magana abar dariya ce domin babu alamun ƙanshin gaskiya a cikinta.

Oduah ta kalubalanci Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed da ya samar da hujjojin da zasu nuna yadda akai take da hannu a cikin sama da fadin da akai da Naira billiyan tara da miliyan dari takwas.

Barayin gwamnati: Ku cire suna na daga ciki

Barayin gwamnati: Ku cire suna na daga ciki

"Duk zargin da suke akai na, a kafar yada labarai babu gaskiya a ciki, kawai siyasa ce. "

A baya-bayan nan ne gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen barayin kasar nan kashi na biyu, da abubuwan da ake zarginsu da shi tare da tabbatar da cewa sai da suka bi diddigi da ƙa'ida kafin wallafa sunayen nasu, kamar yadda Lai Muhammed ya shaida.

Sanatar dai ta bayyana rashin jin dadinta a cikin jawabinta bayan da ta ce an ja hankalinta cewa, sunanta na daga cikin sunayen da Ministan yada labarai ya fitar.

"Abin takaici ne mutum kamarsa (Lai Mohammed) zai fitar da sunayen da yake zargin barayi ne ba tare da cikakken binciken da ya tabbatar da samunsu da laifi ba. Inji Stellah Oduah.

KU KARANTA: Wata mata ta watsawa mijinta ruwan zafi hade da yaji a kan danta

Ta kara da cewa, a ganinta wannan dai wani yunkuri ne na ɓatawa mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen samun nasarori a gwamnatin da ta gabata.

"Sun ce an bayar da kwangiloli ba bisa ƙa'ida ba, a lokacin da nake Minista, amma ni abinda da na sani kawai shi ne, an biya ƴan kwangila kuɗaɗensu kuma sunyi aikinsu. Su je su bincika dukka takardun aikin na nan a adane, ba ni da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da ƴan kwangilar."

Uwargida Stella ta ce, Ina ta zuba idon na ga hujjarsu ko shaida amma har yanzu shiru ban gani ba.

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel