Buhari zai fara hutun shekara a ranar Litinin mai zuwa

Buhari zai fara hutun shekara a ranar Litinin mai zuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa birnin Landan, a ranar Litinin, 9 ga watan Afrilu domin fara hutunsa na shekara, majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da hakan.

A cewar majiyar, shugaba Buhari zai bar kasar da wuri domin ya samu damar hutawa kafin ya halarci taron CHOGM 2018 karo na 25, wanda zaa gudanar a Buckingham Palace, St James’s Palace, da kuma Windsor Castle.

An shirya gudanar da taron ne daga ranar 16-20 ga watan Afrilu.

Buhari zai fara hutun shekara a ranar Litinin mai zuwa

Buhari zai fara hutun shekara a ranar Litinin mai zuwa

Kasar Najeriya na daya daga cikin kasashen Commonwealth, kungiyar da ta hada kasashe 53 dake aiki tare domin kawo ci gaban zaman lafiya da damokradiyya.

KU KARANTA KUMA: Kudaden da ake biyan Sanatoci na tafiyar lamuransu basu saba doka ba - Sanata Sabi

Idan zaku tuna shugaba Buhari ya kwashe tsawon kwanaki 154 a birnin Landan a shekarar 2017 inda ya yi jinya na wata cuta da ba’a bayyana ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel