Kungiyar WANSA ta zabi Buhari a matsayin mamba kwamitin masu bayar da shawara

Kungiyar WANSA ta zabi Buhari a matsayin mamba kwamitin masu bayar da shawara

- Kungiyar kasashen Afirika ta Yamma masu yaki da kananan makamai (WANSA) ta zabi shugaba Muhammadu Buhari a matsayin daya daga cikin mambobinta

- Kungiyar tace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba wai zai kasance mamba kadai ba amma zai zama ciyaman kungiyar

- Kungiyar zata mayar da hankali ne wajen yaki da masu safarar makamai da bindigogi a Afirka ta yamma

Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma masu yaki da kananan makamai (WANSA) ta zabi shugaba Muhammadu Buhari a matsayin daya daga cikin mambobinta. Kungiyar ta bayyana haka a cikin wata takarda data turawa shugaba Buhari a ranar Laraba 21 ga watan Maris.

Kungiyar WANSA ta zabi Buhari a matsayin mamba kwamitin masu bayar da shawara

Kungiyar WANSA ta zabi Buhari a matsayin mamba kwamitin masu bayar da shawara

Legit.ng ta samu labarin cewa WANSA kungiya ce mai zaman kanta wadda ke fada da kananan makamai a yankunan Afirika ta Yamma.

KU KARANTA: Buhari ba zaiyi cacar-baki da Obasanjo ba saboda yana gaba dashi a aikin Soja - Femi Adesina

Kungiyar tace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba wai zai kasance mamba kadai ba amma zai zama ciyaman kungiyar.

Bayan hakan wani cikin ‘Yan Majalissar Wakilai mai wakiltar Dutsinma/Kurfi, Hon. Danlami Mohammed Kurfi a ranar Asabar 31 ga watan Maris, ya bayyana hasashensa na cewa shugaba Buhari zai ci zabe idan har jam’iyyarsu ta APC ta tsayar dashi a zaben 2019, lokacin da yake zantawa da manema labarai.

A wata labarin kuma, dan majalisar wakilai, Honarabul Danlami Mohammed Kurfi ya yi hasashen cewa shugaba Muhammadu Buhari zai lashe zaben shugabancin kasa inda jam'iyyar APC ta tsayar dashi takara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel