Nigerian news All categories All tags
Yan sanda sun damke yan sara-suka 23 a jihar Kaduna

Yan sanda sun damke yan sara-suka 23 a jihar Kaduna

Hukumar yan sandan jihar Kaduna ta alanta cewa jami’anta sun damke akalla yan sara-suka 23 da ke da hannu cikin sharan da ya faru a jihar Kaduna ranan Lahadi.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, Muhktar Aliyu, ya bayyanawa NAN a jihar Kaduna cewa sun damke yan barandan ne misalign karfe 6:30 na yamma a unguwar Kawo.

Yace: “Abinda ya faru shine wani mamban yan daban, Ibrahim Ashiru, ya rasa rayuwarsa bayan ya wanke hannunsa ya fita daga kungiyar daban.

“Sai sauran mambobin suka kai masa hari suka sassareshi. Ya rasa rayuwarsa bayan ai kaishi asibiti.”

Yan sanda sun damke yan sara-suka 23 a jihar Kaduna

Yan sanda sun damke yan sara-suka 23 a jihar Kaduna

Mr Aliyu ya kara da cewa yayinda aka je jana’izar Ashiru, sai wasu kungiyar kuma suka kai harin fansa kan wadanda suka kashe shi.

“Sun garzaya gidajen wadanda suka kashe shi, sun kona gidaje biyu da gidan burodi daya,”.

KU KARANTA: Da ace Shugaba Buhari ya san abin da yake yi da ba haka ba - Obasanjo

Ya ce bisa ga kokarin jami’an yan sanda, an damke mutane 23 kuna an kaddamar da bincike a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel