Nigerian news All categories All tags
EFCC ta gayyaci Okonjo-Iweala don tayi bayani kan yadda aka cire $250m daga kudin Abacha

EFCC ta gayyaci Okonjo-Iweala don tayi bayani kan yadda aka cire $250m daga kudin Abacha

- Tsohuwar Ministar Kudi Ngozi Okonjo Iweala zatayi bayani game da $250m cikin $500m da aka karbo a hannun iyalan tsohon shugaban kasa janar Sani Abacha

- An bayar da kudin ta hanyar Ofishin mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro (ONSA) ba tare da bin ka’idojin da suka kamata ba

- Shugaban hukumar kula da tattalin arziki na kasa mai rukon kwarya, Ibrahim Magu ya bayar da umurnin gayyatar Misis Okonjo-Iweala

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tsohuwar Ministar Kudi Ngozi Okonjo Iweala zatayi bayani game da $250m cikin $500m, da aka karbo a hannun iyalan tsohon shugaban kasa janar Sani Abacha.

Kudin an bayar dasu ne ta hanyar Ofishin mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin tsaro (ONSA) ba tare da bin ka’idojin da suka kamata ba.

Okonjo Iweala zatayi bayani a kan yadda Abacha ya cire $500m daga asusun gwamnati

Okonjo Iweala zatayi bayani a kan yadda Abacha ya cire $500m daga asusun gwamnati

Shugaban hukumar kula da tattalin arziki na kasa mai rukon kwarya, Ibrahim Magu ya bayar da umurnin gayyatar Mrs Okonjo-Iweala don har ma an aika mata da takardar gayyata, bisa ga kudin da aka cire ba tare da wani izini ba a ranar 2, 9, 16, da 18 ga watan Maris, 2015.

NSA ya bayyana cewa babu yanda za’ayi kasa ta cigaba ba tare da kyakyawan tsaro ba, sakamakon haka yayi kira da bayar da tallafin gaggawa ga hukumar tsaro ta kasa.

KU KARANTA KUMA: Kare kai: Kun caccaki Danjuma amma kun yabi sarakuna - Shehu Sani ga gwamnatin tarayya

Akan haka ne aka bayar da $322m don gudanar da ayyukan Soji, sai $700m da aka nema za’a bayar dasu ne fannin ayyukan cigaba.

Okonji-Iweala ta bukaci shugaban kasa ya bayar da umurnin aikawa da kudin Ofishin NSA, amma da sharadin cewa ba duka kudin Abacha da aka karba ne za’a kashe akan siyen makamai ba, sauran za’a zubasu ga fannin cigaban kasa, da kuma cewa kudin za’a nuna aronsu akayi kuma da an samu za’a biya, sannan kuma Ofishin Nsa zasu yiwa shugaban kasa bayani akan yanda akayi da kudaden saboda Ministan kudi baya cikin harkokin tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel