Nigerian news All categories All tags
Kasar Isra'ila zata bawa 'yan Afirka mafaka

Kasar Isra'ila zata bawa 'yan Afirka mafaka

- Gwamnatin kasar Isra'ila ta sanar da fasa korar 'yan gudun hijira 'yan Afirka wadanda Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya dauki kudurin yi, hakan ya biyo bayan zanga-zangar da mutanen yankin suka dinga gudanarwa

Kasar Isra'ila ta fasa korar 'yan gudun hijirar Afirka

Kasar Isra'ila ta fasa korar 'yan gudun hijirar Afirka

Gwamnatin kasar Isra'ila ta sanar da fasa korar 'yan gudun hijira 'yan Afirka wadanda Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya dauki kudurin yi, hakan ya biyo bayan zanga-zangar da mutanen yankin suka dinga gudanarwa.

DUBA WANNAN: Najeriya da kasar Turkiyya zasu hada kai don karfafa hakar soji

Kasar ta Isra'ila ta sanar da cewar, sakamakon amincewa da yarjejeniyar dake tsakanin ta da Majalisar Dinkin Duniya, inda wasu kasashen yamma zasu karbi 'yan gudun hijirar. A karkashin yarjejeniyar da gwamnatin kasar Isra'ilan da Majalisar Dinkin Duniya suka tsara shine, kasashen yamma zasu karbi 'yan gudun hijirar na Afirka akalla dubu 16,250.

Har ila yau, gwamnatin ta amince akan zata bada izinin zama na wucin gadi na shekara 5 ga wasu 'yan gudun hijirar na Afirka kimanin dubu 16 dake kasar ta Isra'ila.

Sanarwar da fadar Firaministan kasar ta Isra'ila ta fitar Benjamin Netanyahu, ta ce za a gabatar da shirin akan mataki guda 3 a cikin shekara 5 inda majalisar dinkin duniya zata rattaba hannu akai.

Gwamnatin kasar ta Isra'ila kuma zata yi kokari wajen ganin ta warware matsalolin da 'yan gudun hijirar ke fuskanta inda ta amince da zata samar musu da sana'o'in yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel