Nigerian news All categories All tags
Gwamna Shettima yayi tir da harin da aka kaiwa kauyukan Borno

Gwamna Shettima yayi tir da harin da aka kaiwa kauyukan Borno

- Shettima ya bayyana harin da aka kaiwa kauyukan karamar hukumar Jere a matsayin zalunci da rashin imani

- Shettima ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara asibitin kwararru dake Maiduguri don ganin mutane 80 da aka raunata lokacin da aka kai harin

- Shettima ya tabbatarwa mutanen cewa gwamnatinsa zata basu kulawa da magunguna kyauta har zuwa lokacin da zasu warke

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa harin da aka kai ranar Lahadi da dare a kauyen karamar hukumar Jere babu tunani ko imani a ciki, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 2 ga watan Afirilu, lokacin da yake zantawa da manema labarai a asibin kwararru na Maiduguri, bayan ya kai ziyara ga mutane 80 da aka raunata lokacin da aka kai harin.

Gwamna Shattima yayi tir da harin da aka kaiwa kauyukan Borno

Gwamna Shattima yayi tir da harin da aka kaiwa kauyukan Borno

Shettima ya bayyana cewa, gwamnatin jiha zata bayar da magunguna kyauta da kuma sauran tallafi ga wadanda harin ya shafa, don a taimakawa majinyatan a zaman da zasuyi na jinya. Gwamnan ya kara da cewa za’ayi duk abunda ya kamata don ganin hakan bai sake aukuwa a kauyukansu ba, ya kumayi gaisuwa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

KU KARANTA: Shugabanin da suka mulki Najeriya tun 1999

kwamishinan ‘Yan Sanda, Damian Chukwu, na jihar Borno ya bayyana cewa, mutane 20 ne aka kashe sai 84 kuma sunji rauni a lokacin harin. Ya kara da cewa an samu gawarwakin ‘yan kunar bakin wake guda biyar sai rigunan bamabamai guda biyu da jami’an suka cire daga wurin da lamarin ya auku.

Legit.ng ta ruwaito cewa Yassine Garba, Mataimakin mai tattara bayanai game da rayuwar mutane na Majalisar Dinkin Duniya (UN) a Najeriya, a ranar Litinin 2 ga watan Afirilu, yayi tir da Allah wadarai ga harin da aka kai a ranar Lahadi a kusada kauyen Belle dake Maiduguri, Borno.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel