Nigerian news All categories All tags
An mayarwa Olusegun Obasanjo martani daga Ofishin Shugaban kasa

An mayarwa Olusegun Obasanjo martani daga Ofishin Shugaban kasa

- Olusegun Obasanjo ya jima yana korafe korafe game da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wanda aka mayar masa da martini cewa ba abun damuwa bane garesu

- Obasanjo ya bayyanawa kungiyar matasa a lokacin da suka kai masa ziyar cewa gwamnatin Buhari ta gaza

- Obasanjo ya shawarci duk ‘yan jam’iyyar APC masu shugabanci a gwamnati dasu daina korafi akan matsalolin da suke fuskanta game da abubuwanda suka tarar na matsaloli

Olusegun Obasanjo ya jima yana korafe korafe game da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wanda aka mayar masa da martini cewa baa bun damuwa bane garesu.

Ya bayyana hakane ga kungiyar matasa a lokacin da suka kai masa ziyar a gidansa, ranar Litinin, 2 ga watan Afirilu, 2018, cewa gwamnatin Buhari ta gaza.

An mayarwa Olusegun Obasanjo martani daga Ofishin Shugaban kasa

An mayarwa Olusegun Obasanjo martani daga Ofishin Shugaban kasa

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa, a Litinin da dare, Obasanjo ya shawarci duk ‘yan jam’iyyar APC masu shugabanci a gwamnati dasu daina korafi akan matsalolin da suke fuskanta game da abubuwanda suka tarar na matsaloli, ya bayyana hakane ga matasan da suka kai masa ziyara a gidansa dake Abeokuta.

KU KARANTA KUMA: Mutane 3 da sunan su ke cikin barayin Najeriya sun fitar da kan su

Ministan Labarai da Al’adun gargajiya, Lai Muhammed yace, gwamnatin tarayya ta APC bazata daina misali da kurakuren gwamnatin adawa data shude ba, saboda tanaso ta magance sake aukuwar irin wadannan kurakuran a gaba.

Babban Mai bawa shugaban kasa shawara, Femi Adesina, yace gwamnatin Buhari ta magance duk matsalolin tattalin arzikin kasar nan, saboda yanzu tana da kudade a asusun ajiyarta na waje wanda bata taba tara kamarsu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel