Nigerian news All categories All tags
Kare kai: Kun caccaki Danjuma amma kun yabi sarakuna - Shehu Sani ga gwamnatin tarayya

Kare kai: Kun caccaki Danjuma amma kun yabi sarakuna - Shehu Sani ga gwamnatin tarayya

- Shehu Sani ya yi sharhi akan matsayar gwamnatin tarayya wajen dubafurucin Danjuma da na wasu sarakuna biyu

- Ya soki lamarin inda yace kamata yayi a duba lamarin ta fuska daya

- Ba wai a caccaki mutun daya sannan a yabama daya ba

Shugaban kwamitin ciwo bashi daga gida da waje na majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani yayi sharhi akan martani daban-daban daga gwamnatin tarayya game da furucin tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, sarkin Birnin Gwari, Malam Zubairu Jibril Mai Gwari II, da kuma sarkin Zamfara akan batun kare kai.

A wani rubutu day a wallafa a shafinsa na twitter a ranar Litinin Sani yace: “Lokacin da Danjuma yayi Magana akan kare kai, kun jefe shi da mashi; lokacin da sarakuna biyu suka yi Magana akan kare kai, kun jefe su da furanni. Ya kamata ace imma ku yabe su tare ko kuma ku Allah wadai da su tare.

Kare kai: Kun caccaki Danjuma amma kun yabi sarakuna - Shehu Sani ga gwamnatin tarayya

Kare kai: Kun caccaki Danjuma amma kun yabi sarakuna - Shehu Sani ga gwamnatin tarayya

“Ba zai yiwu ku mari mutun daya sannan ku lallashi dayana ba a lokacin da suka fada mana yadda muke tsirara”.

KU KARANTA KUMA: Mutane 3 da sunan su ke cikin barayin Najeriya sun fitar da kan su

Ya ci gaba da cewa kira ga kare kai da sarakuna biyu sukayi martini ne ga ci gaban rashin tsaro a fadin kasar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ministan Labarai da Al’adun gargajiya, Lai Muhammed yace, gwamnatin tarayya ta APC bazata daina misali da kurakuren gwamnatin adawa data shude ba, saboda tanaso ta magance sake aukuwar irin wadannan kurakuran a gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel