An kone wani matashi dake sansanin 'yan gudun hijira bisa zargin satar N4,000

An kone wani matashi dake sansanin 'yan gudun hijira bisa zargin satar N4,000

An kone wani matashi dake sansanin 'yan gudun hijira dake garin Ikang a jihar Kuros Riba, ranar Asabar, bisa zarginsa da satar N4,000.

Rahotanni sun bayyana cewar matashin mai shekaru 26 ya bar sansanin 'yan gudun hijirar, mai nisan kilomita 25 daga birnin Kalaba, domin sayen wasu kayayyaki amma sai ya saci kudi a shagon da ya je siyayyar, hakan ya saka wasu matasa yi masa wannan danyen hukunci.

Wani shaidar gani da ido ya ce, "yaje shagon ne domin sayen kayen maye (tsimin tabar wiwi a giya), yayin da matar ta mike domin dauko masa abin da yaje siya, sai ya faki idonta ta dauki jakar ta da take ajiyar kudi ya tsere.

An kone wani matashi dake sansanin 'yan gudun hijira bisa zargin satar N4,000

Sansanin 'yan gudun hijira

Sannan ya cigaba da cewa, "bayan matar tayi ihu ne sai jama'a suka bi shi, bayan sun kwato jakar ne sai suka fara saran shi da adda amma sai taki cinsa, hakan ya saka su zuba masa fetur tare da Cinna masa wuta. Amma duk da haka bai kone ba saida wani mutum ta zuba masa wani gari domin karya duk wani asiri dake jikinsa."

DUBA WANNAN: Hikimar mu ta yin shirin afuwa ga 'yan Boko Haram - Gwamnatin tarayya

Da manema labarai suka ziyarci wurin da abin ya faru a yammacin Asabar din, sun samu gawar matashin a kone a wurin, yayin da mazauna yankin da dama suka tsere domin gujewa kamun 'yan sanda.

Kwamandan sansanin 'yan gudun hijira na Ikang, Effiom Edet, ya ce tuni an shigar da korafi ofishin 'yan sanda dake Ekpri Ikang tare da bayyana cewar matashin ya aikata laifin ne saboda tsananin wuya da ake sha a sansanin ta fuskar rashin isassun kudi da kayan abinci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel