Nigerian news All categories All tags
Yadda ‘Yan sara-suka su ka raunata wani tsohon Soja cikin dare a Kaduna

Yadda ‘Yan sara-suka su ka raunata wani tsohon Soja cikin dare a Kaduna

- Wasu ‘Yan iskan gari da ake kira ‘Yan shara sun addabi cikin Kaduna

- ‘Yan iskan matasa ne ke sare jama’a domin karbe masu kudi da dukiya

- An kira Gwamnati ta kawo karshen wannan barna da ya fitini mutane

Mutanen Karamar Hukumar Kaduna-ta-Arewa a Jihar Kaduna sun shiga rikici bayan da wasu ‘Yan sara-suka su ka shiga ta’adi inda yanzu haka an ji wa wani tsohon Soja rauni yana kwance a babban asibitin Barau Dikko da ke cikin Garin.

Yadda ‘Yan daba su ka raunata wani tsohon Soja cikin dare a Kaduna

‘Yan daba sun ji wa wani Bawan Allah ciwo. Hoto daga: PT

Wadannan ‘Yan sara-suka sun yi barna ne a Unguwar Kwaru Badarawa a Yankin Kawo a Ranar Asabar da kimanin karfe 8:30 kamar yadda Jaridar Premium Times ta bayyana. ‘Yan sara-sukar sun ji wa wannan tsohon Soja rauni ne cikin dare.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tsare wasu mutane da dama a Kaduna

Wannan tsohon Soja mai suna Sani Abdullahi ya dai gamu da ta’adin wadannan ‘yan iskan gari ne lokacin da ya fita sayen burodi. Sani yace a nan-take wani ya daba masa wuka a fuska yayin da wani ya buga masa adda har yanka masa wuyan hannu.

‘Yan sara sukan dai matasa ne ‘yan shekara 18-25 wadanda ake kira ‘yan shara. Mutanen Gari dai na kira Gwamnati su kawo karshen wannan rashin tsaro. Jami’an ‘Yan Sanda dai sun ce sun kama mutane 23 daga cikin ‘Yan sharan a cikin Unguwar Kawo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel