Nigerian news All categories All tags
2019: Saraki ya karyata jita-jitar fitowa takarar shi da ake yi

2019: Saraki ya karyata jita-jitar fitowa takarar shi da ake yi

- A ranar Litinin dinnan ne Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Bukola Saraki, ya karyata ikirarin da ake yi akan shi na cewar yana neman kujerar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa na 2019. Mista Saraki, dan majalisar dattijai na jam'iyyar APC mai mulki, ya ce jita-jitar da ake yadawa akan shi na cewar zai fito takarar shugaban kasa karya ce

2019: Saraki ya karyata jita-jitar fitowa takarar shi da ake yi

2019: Saraki ya karyata jita-jitar fitowa takarar shi da ake yi

A ranar Litinin dinnan ne Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Bukola Saraki, ya karyata ikirarin da ake yi akan shi na cewar yana neman kujerar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa na 2019. Mista Saraki, dan majalisar dattijai na jam'iyyar APC mai mulki, ya ce jita-jitar da ake yadawa akan shi na cewar zai fito takarar shugaban kasa karya ce.

DUBA WANNAN: Barayin Gwamnati: Babu wanda ya bani N1.6b da ake zargi na dashi - Mu'azu Babangida Aliyu

A wata hira da manema labarai suka yi da mai bashi shawara a harkar sadarwa, ya ce babu alamun gaskiya a cikin jita-jitar da ake yadawa. A kwanakin baya ne wata jarida mai suna "The Boss" ta rawaito cewar Saraki yana son fitowa takarar shugaban kasa a zaben da za a gabatar na shekarar 2019.

"Babu shakka na san cewar gwamnatin APC baza ta iya cigaba da mulki ba batare da Saraki ba, domin kuwa kuwa a duk 'yan siyasar kasar nan, babu wanda yake da jajircewar shi da kuma ilimi akan harkar siyasa.

"Wasu majiyoyi marasa tushe sun yada cewar Saraki yana son fitowa takarar shugabancin kasar, shine yasa yake so ya kulla dangantaka mai karfi tsakanin shi da manyan kasar nan."

Sai dai Mista Olaniyonu ya ce rahoton ba haka yake ba. yace inda da gaske ne cewa yana son fitowa takara, da tuni an fitar da rahoton hakan a cikin manya-manyan kafafen sadarwa na kasar nan. Amma kamar yanda kuka gani, babu wani abu makamancin haka, inji Mista Olaniyonu.

Har ila yau, wani rahoton kuma ya nuna cewa Mista Saraki, yana son ya dauki mataimakin shi na majalisar dattijai Mista Ike Ekweremadu a matsayin wanda zaiyi mashi mataimakin shugaban kasa.

A shekarar 2011, Saraki ya nuna sha'awar shi ta fitowa takarar shugaban kasar nan a karkashin jam'iyyar PDP, sai kuma aka samu akasi aka bawa Atiku Abubakar damar fitowa takarar daga yankin arewa. Inda daga baya ya hada baki da sauran 'yan jam'iyyar PDP din aka cire tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, aka bawa shugaba Muhammadu Buhari kujerar shugabancin kasar.

Har yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari bai bayyana burin shi na sake fitowa takara ba a karo na biyu, sai dai alamu sun nuna cewar shugaban zai bayyana manufar tasa nan bada dadewa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel