Kudin da na kashe a zaben 2015 ba na sata bane inji Femi Fani-Kayode

Kudin da na kashe a zaben 2015 ba na sata bane inji Femi Fani-Kayode

- Femi Fani Kayode yayi wa Lai Mohammed raddi na cewa ya saci kudi

- Fani Kayode yace kudin da ya kashe wajen kamfe ba na Gwamnati bane

- Tsohon Ministan yace zai dai cigaba da kare kan shi da Iyalin sa a Kotu

Mun samu labari cewa tsohon Ministan kasar nan a lokacin Shugaban kasa Olusegun Obasanjo kuma babban ‘Dan Jam’iyyar adawa na PDP Femi-Fani Kayode ya bayyana abin da ya faru a 2015 wajen yakin neman zaben Shugaban kasa.

Kudin da na kashe a zaben 2015 ba na sata bane inji Femi Fani-Kayode

Fani-Kayode ya fadawa Gwamnatin APC bai saci Miliyan 866 ba

Babban ‘Dan adawar Gwamnatin Shugaban kasa Buhari Fani-Kayode bai ji dadi bayan da ya ji sunan shi cikin jerin barayin kasar nan ba da Ministan yada labarai da Mista Lai Mohammed ya saki a cikin karshen makon da ya wuce.

KU KARANTA: Stella Oduah ta caccaki Gwamnatin Shugaba Buhari

Femi Kayode yana cikin kusoshin da su ka tsaya wajen ganin Goodluck Jonathan ya zarce a 2015 inda ya nuna cewa Naira Miliyan 800 da su ka shigo hannun sa na yakin neman zaben PDP sam ba daga asusun Gwamanti su ka fito ba.

Tsohon Ministan yace maganar banza ne ace ya saci wadannan makudan miliyoyi alhali tsohuwar Sanatan PDP Nenedi Esther ce ta mika masa wannan kudi domin ganin ‘Dan takarar PDP Goodluck Jonathan ya koma kujeran sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel