Nigerian news All categories All tags
2019: Jam’iyyar APC za ta samu gagarumar nasara – Inji Ima Niboro

2019: Jam’iyyar APC za ta samu gagarumar nasara – Inji Ima Niboro

- Ima Niboro yace Jam'iyyar APC ce za ta lashe zabe mai zuwa

- Kakakin Jonathan a0da yace Jama'a na neman canji a Kasar

- Niboro ya komo Jam'iyyar APC bayan ya bar Gwamnatin PDP

Wani tsohon mai magana da yawun bakin tsohon Shugaba kasa Goodluck Jonathan watau Ima Niboro ya bayyana cewa duk a je a dawo dai Jam'iyyar APC ce dai za ta lashe zaben da za ayi a shekarar 2019.

2019: Jam’iyyar APC za ta samu gagarumar nasara – Inji Ima Niboro

Mista Niboro ya koma APC ne a 2016 a Jihar Delta

Ima Niboro ya bayyanawa manema labarai a karshen wannan makon cewa APC za ta samu gagarumar nasara a 2019 domin mutanen kasar nan na neman canji a halin yanzu. Niboro dai ya yarda cewa akwai 'yan matsaloli a Jam'iyyar.

KU KARANTA: Yadda kakakin Majalisar dokokin Kano ya sulhunta rikicin Jihar

Mai magana da bakin Jonathan a-baya yace zaben da aka yi na kananan Hukumomi kwanan nan a Jihar sa ta Delta ya nuna cewa APC na iya lashe zaben Gwamnan Jihar inda yayi kira da 'Yan Jam'iyyar a Jihar da su kara hakuri dai.

Niboro ya nuna cewa babu abin da ya dace da Jama'a irin su shiga Jam'iyyar APC mai mulkin Kasar domin ganin an kawo gyara a Jihar Delta. Ima Niboro ya komo Jam'iyyar APC ne a 2016 bayan ya rike Shugaban Hukumar NAN na kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel