Nigerian news All categories All tags
Mutane 18 ne suka hallaka a harin Boko Haram

Mutane 18 ne suka hallaka a harin Boko Haram

Yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun hallaka akalla mutane 18 da jikkata da yawa a wani mumunan harin da suka kai sansanin soji da kuma kauyukan da ke makwabtaka da wajen.

Yan Boko Haram din sun kai farmaki barikin sojin ne tare da yan kunar bakin wake inda sukayi artabu da soji na dan lokaci.

Wani babban jami’in soja yace: “Yan Boko Haram 18 sun kawo hari barikin yan sanda yayinda yan kunar bakin wake 7 suka kai hari kauyukan Bale Shuwar da Alikaranti misalign karfe 8:50 na dare.”

Mutane 18 ne suka hallaka a harin Boko Haram

Mutane 18 ne suka hallaka a harin Boko Haram

Wani jami’in hukumar bada agaji na gaggawa SEMA, Bello Dambatto yace: “Zuwa yanzu mun ga gawawwaki 18 daga kauyuka biyun.

An kashesu ne yayinda suke kokarin arcewa daga wajen musayar wuta tsakanin soji da yan Boko Haram.”

KU KARANTA: Matashi ta hallaka yayansa saboda ya bashi shawara akan shan barasa

Soja daya ya hallaka amma dai an hallaka yan Boko Haram 6 kuma an dakile yan kunar bakin wake 7.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel