Yansanda sun cafke yan sara suka 23 da suka kashe wani tare da kona gidaje a Kaduna

Yansanda sun cafke yan sara suka 23 da suka kashe wani tare da kona gidaje a Kaduna

Rundunar Yansandan jihar Kaduna ta bayyana cewar jami’anta sun kama wasu yan sara suka guda 23 da ake yi ma lakabi da suna ‘yan shara’ dake da hannun cikin kashe wani mutumi da kona gidaje.

Kamfanin dillancin labaru,NAN, ta ruwaito Kaakakin rundunar ASP Aliyu Mukhtar ya bayyana cewa da misalin karfe 6:30 na rana ne Yansandan suka kai samame a unguwar Kawo, inda aka yi wani tashin tashina da yayi sanadin mutuwar wani matashi Ashiru Ibrahim.

KU KARANTA: Bashin naira Triliyan 4.2: Majalisun dokokin Najeriya na gab da watsa ma Buhari kasa a ido

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin yana cewa: “Yan sharan sun kashe wani matashi ne mai suna Ibrahim Ashiru mai shekaru 27 a unguwar Kawo bayan ya bayyana musu ya daina harkar sara suka, ya tuba.”

Sai dai Kaakakin yace bayan an binne Ashiru ne sai wasu Gungun yan sara suka na daban suka kai harin daukan fansa, inda suka shiga neman wadanda suke zargin na hannu cikin kisan Ashiru, da basu same su ba, sai suka babbaka gidajensu guda biyu da wani gidan Burodi.

Amma cikin ikon Allah da zuwan Yansanda, suka kaddamar da wani samame, ba tare da bata lokaci ba suka kama mutaen 23. A yanzu haka an fara gudanar da bincike, inji Kaakaki Aliyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel