Nigerian news All categories All tags
Shawara ba ciwo bane: Matashi ta hallaka yayansa saboda ya bashi shawara akan shan barasa

Shawara ba ciwo bane: Matashi ta hallaka yayansa saboda ya bashi shawara akan shan barasa

Hukumar yan sandan jihar Neja ta damke matashi dan shekara 25 mai suna, Dodo Baraje, kan laifin kisan babban yayanshi bayan saboda ya bashi shawara.

Dodo Baraje wanda yayi Magana da manema labarai kan abun takaicin da ya faru a kauyen Shirumbu ya bayyana cewa ya harbe yayansa ne cikin fushi saboda ya bugesa don yana shan madarar ‘Sukodaye’.

Majiyar Northern City News ya tattara cewa matashin ya kasance yana zama da yayan nasa ne kafin yanzu. Jami’an yan sanda sun yi ram da shi ne yayinda yake kokarin arcewa.

Shawara ba ciwo bane: Matashi ta hallaka yayansa saboda ya bashi shawara akan shan barasa

Shawara ba ciwo bane: Matashi ta hallaka yayansa saboda ya bashi shawara akan shan barasa

Yace: “Cikin fushi na shiga gida dauko bindiga na harbe shi… Ban taba tunanin zai mutu ba. Kawai yana min fada ne domin in zama mutumin kwarai kuma iyalina suyi alfahari da ni, na mutu na lalace.

Ina cikin maye ne lokacin, da ba zan kashe yayana wanda ya kula da nib a. Ban taba fada da shi ba, na rantse ba san abinda yah au kaina ba. Allah ya gafarta min.”

KU KARANTA: Barayi da masu garkuwa da mutane 750 sun tuba

Yayin tabbatar kama wannan mashi, kakakin hukumar yan sandan jihar, Muhammad Abubakar, ya ce za’a gurfanar da shi a kotu ba da dadewa.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel