Siyasar Kano: Kaakakin majalisa ya bayyana dabarar da yayi wajen hada kan Kwankwasiyya da Gandujiyya

Siyasar Kano: Kaakakin majalisa ya bayyana dabarar da yayi wajen hada kan Kwankwasiyya da Gandujiyya

Kaakakin majalisar dokokin jihar Kano, Yusuf Abdullahi Ata yayi karin haske game da dabarun da yake bi wajen magance rarrabe rarraben kawuna a tsakanin mabiya Gandujiyya da Kwankwasiyya a majalisar dokokin jihar.

Ata ya bayyana haka ne a cikin shirin ‘Barka da war haka’ na gidna rediyon Freedom Kano, inda yace ya samu nasarar kashe wutar rikicin siyasar Kwakwansiyya da Gandujiyya a majalisar ne ta hanyar jan kowa a jiki.

KU KARANTA: Wani fitaccen Malamin Izala ya ɗaura ɗamarar ƙwato wata muhimmiyar mukamin siyasa a Kano

“Ina baiwa kowa hakkinsa a majalisa, musamman duk abinda ya shafi tattauna kudururruka a majalisar, ina kokarin ganin cewa kowa ya tofa albarkacin bakinsa a ciki, hakan ne kadai zai kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a majalisar.

“Adalcin da nake yi ma dukkanin yan majalisun yasa yan Kwankwasiyya basa kawo cikas da duk wasu bukatun gwamnatin gwamna Abdullahi Ganduje da ya kawo majalisar don neman izini.” Inji Kaakaki.

Sai dai Kaakakin yace zuwa yanzu sun gabatar da kuduri guda hudu da har sun zama sahhalewar gwamnatin jihar, inda suka zama doka, da suka danganci kyautata kiwon lafiyar al’ummar jihar Kano.

Daga cikin dokokin akwai, dokar asusun kiwon lafiya na jihar Kano 2017, dokar gudanar da asibitoci masu zaman kansu, dokar asusun gata na kiwon lafiya da kuma dokar kafa manyan asibitoci na zamani guda biyu a Kano, asibitin Muhammadu Buhari dake Giginyu da Asibitin yara dake titin gidan Zoo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel