Nigerian news All categories All tags
Bashin naira Triliyan 4.2: Majalisun dokokin Najeriya na gab da watsa ma Buhari kasa a ido

Bashin naira Triliyan 4.2: Majalisun dokokin Najeriya na gab da watsa ma Buhari kasa a ido

Alamu karara sun bayyana game da wata sabuwar kitimurmura da yan majalisun dokokin Najeriya suka shirya ma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa wata bukata da Buhari ya mika musu.

Vanguard ta ruwaito yan majailisar dattawa, wato Sanatoci ne suka fara yanke shawarar daukan wannan mataki, daga bisanu kuma yan majalisar wakilai suka bi sawunsu, inda suka shirya yin watsi da umarnin neman cin bashin naira Triliyan 4.2 da Buhari ya aiko musu.

KU KARANTA: Jami’an rundunar Yansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane guda 5 a Taraba

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan majalisun sun yanke wannan shawarar ne duba da yadda suka ce shugaban kasa da mukarrabansa na bangaren zartarwa basa muntata bangaren majalisun dokokin kasar nan.

Bashin naira Triliyan 4.2: Majalisun dokokin Najeriya na gab da watsa ma Buhari kasa a ido

Buhari a majalisa

A bayan Yan majalisar bayan sun amince ma gwamnati ciyo bashin naira Triliyan 9.2 a shekarar 2016, sun nemi ta basu bahasi kan yadda ta kashe kudaden, amma har yanzu shiru kake ji kamar mushrik yaci shirwa ya sha ruwa.

Yan majalisun sun zargi Buhari da nuna halin ba’a tare ga majalisun dokokin kasar nan, don haka su ma a yanzu shun kammala shirin watsa masa kasa a idanu ta hanyar hana shi bukatar da ya gabatar a gabansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel