Nigerian news All categories All tags
Wata sabuwa: Kungiyar Boko Haram ta kai hari Maiduguri sun kashe mutane 15 tare da raunata wasu 55

Wata sabuwa: Kungiyar Boko Haram ta kai hari Maiduguri sun kashe mutane 15 tare da raunata wasu 55

- Boko Haram sun sake kai hari a wani kauye mai suna Bale, inda suka hallaka mutane 15 suka kuma raunata wasu mutane 55

- An samu labarin cewa an dauki awowi ana jin karar harbin bindiga da tashin bamabamai daga kauyen dake kusa da garin

- Wani daga cikin jami’an tsaro ya fadawa manema labarai cewa sunyi yunkurin mamaye kauyukan da suka kai harin ne na kusa kusa da Maiduguri

Boko Haram sun sake kai hari a wani kauye mai suna Bale-Suwa da kuma Bale kura,wandanda ke kusa da garin Maiduguri, a daren ranar Lahadi, 2 ga watan Afirilu, 2018, inda suka hallaka mutane 15 suka kuma raunata wasu mutane 55.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta samu labarin cewa an dauki awowi ana jin karar harbin bindiga da tashin bamabamai daga kauyen dake kusa da garin, a ranar ta Lahadi, inda wani daga cikin jajirtattun jami’an tsaro ya fadawa NAN cewa sunyi yunkurin mamaye kauyukan ne a lokacin da suka kai harin a ranar, da misalin karfe 8 na dare.

Majiya ta bayyana cewa sun ajiye ababen hawansu daga nesa da inda jami’an tsaro masu kula da hanya suke, suka lababa suka shiga kauyukan, inda jami’an tsaron suka sha gwagwarmaya dasu lokacin da suka samu labara suka kai dauki.

KU KARANTA KUMA: Tsare-tsare game da yanda akeso a dakatar da Magu daga aiki sun bayyana

Duk da cewa kwamandan rundunar Sojin na Lafiya Dole wadanda suka kai daukin, Manjo Janar Rogers Nicholas, ya musanta maganganu a kan mutuwar mutanen kauyukan ko jami’ansa, sai dai ya bayyana cewa su wadanda suka kai harin ne aka kashe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel