Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: An damke dan barandan karshe mai wa Dino Melaye aiki da ya tsere daga kurkuku

Yanzu-yanzu: An damke dan barandan karshe mai wa Dino Melaye aiki da ya tsere daga kurkuku

Kabiru Seidu wanda aka fi sani da Osama, na karshe cikin yan barandan da ke da alaka da Dino Melaye, ya dawo hannu.

Kabiru Seidu tare da wasu 6 sun arce daga kurkukun yan sanda ne ranan Laraban da ya gabata yayinda ake shirin gurfanar da su a gaban kotu ranan.

Osama, Nuhu Salisu a.k.a Small, Aliyu Isa, Adams Suleiman, Emmanuel Audu da Musa Mohammed sun arce daga kurkukun jami’an SARS ne a Lokoja jihar Kogi.

Yanzu-yanzu: An damke dan barandan karshe mai wa Dino Melaye aiki da ya tsere daga kurkuku

Yanzu-yanzu: An damke dan barandan karshe mai wa Dino Melaye aiki da ya tsere daga kurkuku

An damke Kabiru ne da daren Lahadi a jihar Bauchi kuma tuni an garzaya da shi birnin tarayya Abuja. Majiyan hukumar yan sanda sun bayyana cewa yanzu dai sun damke dukkan masu aiki da sanata Dino Melaye da suka arce daga kurkuku.

KU KARANTA: Jami’an rundunar Yansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane guda 5 a Taraba

Tun lokacin da aka damke yan barandan a kwanakin nan, Melaye bai sake magana ba duk da cewan ya baiwa sifeton yan sanda wa'adin damko yan barandan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel