Duk wanda ke korafi kan yunwa yaje ya nemi aikinyi - Hadimin Buhari

Duk wanda ke korafi kan yunwa yaje ya nemi aikinyi - Hadimin Buhari

- Babban mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin sadrwa ga jama’a Garba shehu, yace “duk wanda ke korafi a kan yunwa yaje yayi aiki”

- Lokacin da yake zantawa da Ben TV, Shehu yace, wanndan gwamnatin ta bayar da jari ga muta mutane da kuma ayyukan cigaba a kasar nan

- Shehu yace tun lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya karba mulki a shekarar 2015 ya bayar da sama da 30% na dukiyar kasar nan ga fannin ayyukan cigaba

Babban mai bawa shugaban kasa shawara ta fannin sadarwa, Garba shehu, yace “duk wanda ke korafi a kan yunwa yaje yayi aiki”.

Lokacin da yake zantawa da Ben TV, Shehu yace, wanndan gwamnatin ta bayar da jari ga mutane da kuma ayyukan cigaba a kasar nan.

Yace: “wannan gwamnatin ce kadai ta kawo ayyukan cigaba wadanda ke bawa talakawa tallafi, inda a kalla abunda zaka samu isan kayi aiki shine 5,000, wanda da yawa daga cikin ayyukan nan samar dasu ne ta hanyar bayar da bashi daga babban banki na tarayya, ko bankin maikatu, ko bankin harkokin noma, ko na cigaba, ko makamantansu, wanda ribar kadance wani ma ba ribar.

Duk wanda ke korafi kan yunwa yaje ya nemi aikinyi - Hadimin Buhari

Duk wanda ke korafi kan yunwa yaje ya nemi aikinyi - Hadimin Buhari

Shehu yace tun lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya karba mulki a shekarar 2015 ya bayar da sama da 30% na dukiyar kasar nan ga fannin ayyukan cigaba. Ya kara da cewa kasa bazata taba cigaba ba inba ana gudanar da ayyukan cigaban yanda ya kamata ba.

“Akwai takardu na shaida wadanda zasu tabbatar da cewa babu wata gwamnati da aka tabayi a kasar nan data taba bayar da tallafi mai yawan wannan da muka bayar a tarihin Najeriya ko ince muke cikin bayarwa a bagaren ayyukan cigaba” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Dole mu bawa matasanmu karfin gwiwa na su karbi jagorancin Najeriya - IBB

“30% na arzikin kasar nan yana tafiya ne ta fannin ayyukan cigaba wanda an sameshi sosai a kasar nan. A yanzu haka akwai ayyuka dama da ake gunarwa kamar na ayyukan hanyoyin jiragen kasa sababbi da akeyi da kuma tsofaffi da ake gyarawa, wand aba sai an fada maka ba”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel