An yi ta jin harbe harbe da karar fashewar wasu abubuwa a Maiduguri

An yi ta jin harbe harbe da karar fashewar wasu abubuwa a Maiduguri

Labari dake zuwa mana daga garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno ya nuna cewa al’umma sun ji karan harbe-harben bindiga da kuma fashewar wasu abubuwa a daren ranar Litinin.

Wasu majiyoyi na tsaro sun ce sojoji ne ke artabu da wasu yan ta’addan Boko Haram a wajen birnin.

Zuwa yanzu dai babuwani cikakken bayani game da adadin mutanen da al’amarin ya rutsa da su.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jami’an Soji dake gudanar da aikin bincike na Ayem Akpatuma, a jihar taraba tare da jami’an ‘Yan Sanda, a ranar 31 ga watan Maris 2018, sunyi nasarar kama wasu ‘yan ta’adda dake ta’addanci a garin Mayo Ndaga, inda aka samesu da fallayen kwanon rufi, gado da kuma bindigar kugu ta hausa.

KU KARANTA KUMA: Dole mu bawa matasanmu karfin gwiwa na su karbi jagorancin Najeriya - IBB

Jami’an sunyi nasarar kama wasu ‘yan ta’addan, Palat Jafainal mai shekaru 20, da Kingsiley Benson mai shekaru 25, inda suma aka samesu da kayayyaki wanda suka hada da fallayen kwanon rufi, da keken dinki, da injinan bayar da wutar lantarki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel