Nigerian news All categories All tags
Shugaban sojin sama ya jagoranci kungiyar Sojin a arewa maso gabas (hotuna)

Shugaban sojin sama ya jagoranci kungiyar Sojin a arewa maso gabas (hotuna)

- Shugaban Sojin Sama ya shiryawa Sojin dake gwagwarmaya a arewa maso gabashin Najeriya biki lokacin da suka kaiwa iyalansu ziyara

- Shugaban wanda kwamandan kula da ayyuka (ATF) na Lafiya Dole, da mataimakin shugaban (AVM) Idi Lubo, suka wakilta, sunyi jinjina ga Sojin bisaga irin gagarumar gudunmuwar da suka bayar wurin magance tashe tashen hankula a kasar nan

- Yace duk da nasarorin da aka samu akan kungiyar Boko Haram, jami’an kada su kara bada kwazo wurin ganin an magance ta’addanci a kasar nan baki daya

Shugaban Sojin Sama ya shiryawa Sojin dake gwagwarmaya a arewa maso gabashin Najeriya biki lokacin da suka kaiwa iyalansu ziyara a lokacin Easter.

Shugaban wanda kwamandan kula da ayyuka (ATF) na Lafiya Dole, da mataimakin shugaban (AVM) Idi Lubo, suka wakilta, sunyi jinjina ga Sojin bisaga irin gagarumar gudunmuwar da suka bayar wurin magance tashe tashen hankula a kasar nan.

Shugaban sojin sama ya jagoranci kungiyar Sojin a arewa maso gabas (hotuna)

Shugaban sojin sama ya jagoranci kungiyar Sojin a arewa maso gabas

Yace duk da nasarorin da aka samu akan kungiyar Boko Haram, jami’an kada su kara bada kwazo wurin ganin an magance ta’addanci a kasar nan baki daya.

Bayan nan wakilan sun ci abincin rana tare da wasu jami’an dake aiki a garin Yola.

Shugaban sojin sama ya jagoranci kungiyar Sojin a arewa maso gabas (hotuna)

Shugaban sojin sama ya jagoranci kungiyar Sojin a arewa maso gabas

AVM Lubo yayi godiya ga shugaban Sojin (AM) Abubakar bisa ga irin wannan kulawa daya nuna ga jami’an.

Bayan haka Lubo yayi jinjina garesu suma bisa ga nasu kokarin na aiki ba dare ba rana don magance rashin tsaro a kasar.

Shugaban sojin sama ya jagoranci kungiyar Sojin a arewa maso gabas (hotuna)

Shugaban sojin sama ya jagoranci kungiyar Sojin a arewa maso gabas

Ya kuma bukaci su kara jajircewa don ganin cewa sun kawar da rashi tsaro daga yankin.

KU KARANTA KUMA: Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba

AVM Lubo ya kuma gabatar da kyaututtuka ga jajirtattun jami’an wanda aka bawa jagoransu Captin Samuel Eyoma, shugaban kungiyar tattara bayanai.

Daga karshe ya kuma yi kira ga sauran kungiyoyin jami’an da suyi koyi da Eyom. Sannan ya kaddamar da aikin wurin ajiyar kayan aiki na Sojin a sansanin 103, a garin Yola.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel