Nigerian news All categories All tags
Dole mu bawa matasanmu karfin gwiwa na su karbi jagorancin Najeriya - IBB

Dole mu bawa matasanmu karfin gwiwa na su karbi jagorancin Najeriya - IBB

- Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soji, Ibrahim Basamasi Babangida yace Dattawa sun dade suna jagorancin kasar nan ya kamata su bawa matasa donsu jagoranci kasar suma

- Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakane lokacin da kungiyar cigaban siyasa suka kai masa ziyara a fadarsa dake dake garin Minna

- IBB ya bayyana cewa sun dade suna shawarar yanda za’a bawa matasa mulkin kasar nan tun shekarar 1989

Tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin Soji, Ibrahim Basamasi Babangida yace tsofaffi sun dade suna jagorancin kasar nan ya kamata su bawa matasa dama donsu jagoranci kasar suma daidai da yanda zamani ke tafiya.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakane, a ranar Lahadi, lokacin da kungiyar cigaban siyasa, mai lakabi da New Nageria, wadda Moses Siloko ke jagoranta, suka kai masa ziyara a gidansa dake dake garin Minna.

IBB ya bayyana cewa sun dade suna shawarar yanda za’a bawa matasa mulkin kasar nan tun shekarar 1989 don kawo cigaba a kasar, amma Dattawa suka hana.

IBB ya bayar da misali da Tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon, wanda ya mulki Najeriya da shekaru 30, wanda ya kokarta wurin hadin kan kasa da cigaban kasa baki daya wanda har yau ana cin moriyar aikinsa.

Dole mu bawa matasanmu karfin gwiwa na su karbi jagorancin Najeriya - IBB

Dole mu bawa matasanmu karfin gwiwa na su karbi jagorancin Najeriya - IBB

Tsohon shugaban kasar na mulkin Soji ya bayyana cewa yayi matukar farin ciki lokacin da yaji an kafa dokar bawa matasa damar yin mulki a majalisar zartarwa, yace “wasu daga cikinmu sun amince da wannan shawara kuma zasu mara mata baya”.

Mista Siasia wanda ke shugaban jam’iyyar PDM yace “mun kaiwa tsohon shugaban kasar ziyara ne don ya sanya musu albarka."

Ya kara da cewa lokaci yayi da matasa zasu tashi donsu karbi mulkin kasar nan tinda dattawan sun kasa.

KU KARANTA KUMA: Jami’an Soji sun kama wasu gagaruman ‘yan ta’adda a jihar Taraba

A ranar Litinin kuma zamu kaiwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ziyara a gidansa dake Otta, daga bisani zamu wuce gurin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan tare da tsohon shugaban kasa Abdulsam Abubakar ziyar don suma susa tasu albarkar”, inji shi. yake dashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel