Hikimar mu ta yin shirin afuwa ga 'yan Boko Haram - Gwamnatin tarayya

Hikimar mu ta yin shirin afuwa ga 'yan Boko Haram - Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya, ta bakin mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Garba Shehu, ta bayyana cewar yin shirin yin afuwa ga mayakan kungiyar Boko Haram zai kawo karshen zubar da jini da asarar kudi da kasa ke yi.

Kazalika, fadar ta shugaban kasa ta bayyana cewar shugaba Buhari ya yi shiru a kan batun sake tsayawa takara ne saboda ya fi mayar da hankali wajen gudanar da aiyukan da zasu ciyar da kasa gaba.

Da yake ganawa da manema labarai a Abuja, Garba Shehu, ya ce aiyukan da shugaba Buhari ya shimfida zasu bashi nasara a zaben shekarar 2019.

Hikimar mu ta yin shirin afuwa ga 'yan Boko Haram - Gwamnatin tarayya

Mallam Garba Shehu

Mallam Shehu ya ce koda dukkan tsofin shugabannin kasar nan da suka bawa Buhari shawarar kada ya tsaya takara, zasu hadu wuri guda su tsaya takarar shugabancin kasa, Buhari zai kayar da su.

DUBA WANNAN: An Sace Amarya Da Y'an Rakiyar ta 10 Kan Hanyar su Ta Zuwa Gidan Angonta

Da yake mayar da martani a kan zargin cewar shugaba Buhari ya yi shiru a kan aiyukan ta'addanci da makiyaya ke tafkawa a wasu sassan Najeriya, Mallam Shehu, ya musanta bayar da kariya ga kowacce kungiyar ta'addanci tare da bayyana cewar gwamnatin tarayya na shirin yin afuwa ga 'yan ta'adda dake shirin ajiye makamansu.

Ya kara da cewar, yin hakan zai kawo karshen zubar da jini da kuma kashe makudan kudi da gwamnatin tarayya keyi a bangaren tsaro.

Garba Shehu ya ce, hatta kasashen da suka fi Najeriya cigaba a duniya na rungumar tsarin yin afuwa ga 'yan ta'adda domin kawo karshen zubar da jini ta hanya mai sauki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel