Zaben Gwamna: Kayode Fayemi ya zari takobin komawa kujerar sa

Zaben Gwamna: Kayode Fayemi ya zari takobin komawa kujerar sa

- Ministan ma’adanai Kayode Fayemi yace zai nemi takarar Gwamnan Ekiti

- Dr. Fayemi yayi mulki a Jihar Ekiti daga 2010 har zuwa 2014 da ya fadi zabe

- Ayo Fayose na kokarin ganin dai Fayemi bai dawo kan kujerar da ya bari ba

Mun samu labari cewa Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti kuma Ministan ma’adanai a Gwamnatin Shugaban kasa Buhari watau Dr. Kayode Fayemi ya shirya komawa kujerar sa na Gwamna a wannan shekarar bayan ya sha kasa a zaben 2014.

Zaben Gwamna: Kayode Fayemi ya zari takobin komawa kujerar sa

Kayode Fayemi na neman karbe kujerar sa daga Gwamna Ayo Fayose

Kwanan nan ne Kayode Fayemi yayi hira da ‘Yan jarida a gaban magoya bayan sa yayin da ya kai ziyara zuwa Kauyen sa a Jihar Ekiti inda ya tabbatar masu da cewa zai nemi takarar Gwamnan Jihar a zaben da za ayi a tsakiyar shekarar nan.

KU KARANTA: Masu neman takarar Gwamnan Jihar Ekiti sun karu

Fayemi yace zai fara sanar da Hukumar zabe na INEC game da shirin sa na tsayawa takara sannan kuma yace zai bayyanawa Jam’iyyar su ta APC matsayar sa. Manyan Jam’iyyar APC a Jihar da dama dai sun ce su na tare da Ministan kasar.

Kwanaki dai Gwamnatin Jihar ta haramta masa tsayawa takara sai dai ya nuna cewa Gwamna Ayo Fayose bai isa ya hana sa neman Gwamna ba. Fayemi ya kuma yi alkawarin dawowa da kananan Hukumomin da Fayose ya ruguza a 2014.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel