Nigerian news All categories All tags
Zaben 2019: Bukola Saraki zai nemi kujerar Shugaba Buhari

Zaben 2019: Bukola Saraki zai nemi kujerar Shugaba Buhari

- Akwai jita-jitar cewa Saraki zai yi takara da Shugaba Buhari a 2019

- Sai dai wasu na ganin aikin wasu makiya ne kurum a Jam’iyyar APC

- Har yanzu dai Shugaban Majalisar bai tabbatar da wannan magana ba

Mun samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yana shirin tsayawa takarar Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019. Sai dai wasu sun ce an fara yada labari ne kurum domin a hura wutar rikicin Jam’iyyar APC.

Zaben 2019: Bukola Saraki zai nemi kujerar Shugaba Buhari

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki zai tsaya takara

Jaridar Boss ta fara rahoto cewa Bukola Saraki zai nemi takara a 2019 sai kuma ga shi an ji Shugaban gidan Jaridar Ovation watau Dele Momodu yana kiran jama’a su marawa Shugaban Majalisar kasar baya a zabe mai zuwa domin yace ya cancanta.

KU KARANTA: Adamu Garba yace zai gwabza da Buhari a zaben 2019 a APC

Sai dai wata Majiya daga Jaridar This Day tace an fara yada wannan jita-jita ne domin a hada rikici a Jam’iyyar yayin da maganar kujerar Shugaban APC na kasa John Oyegun take cigaba da rawa amma babu gaskiya a maganar takarar Saraki.

Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki ya nemi takarar Shugaban kasa tun ba yau ba, kuma ko a zaben da ya wuce yayi kokarin tsayawa takarar kafin ya yanke shawarar komawa Majalusa. Har yanzu dai Saraki bai ce komai ba game da maganar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel