Sanata Shehu Sani ya kara rubutawa Buhari wasika a karo na biyu, ya bashi wata shawara

Sanata Shehu Sani ya kara rubutawa Buhari wasika a karo na biyu, ya bashi wata shawara

Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Shehu Sani, ya sake aike da wani sako ga shugaba Buhari a karo na biyu cikin sati guda.

Sanatan ya aike da sakon ne biyo bayan barkewar cece-kuce a kan wata kyauta da gidauniyar tsohon mai fafutikar neman 'yan bakaken fata a kasar Amurka, Martin Luther king (MLK), ta bawa shugaba Buhari.

An samu barkewar cece-kucen ne bayan kungiyar ta MLK ta musanta bawa shugaba Buhari wata kyauta.

Sanata Shehu Sani ya kara rubutawa Buhari wasika a karo na biyu, ya bashi wata shawara

Sanata Shehu da Buhari

A wani gajeren sako da ya aike ga shugaba Buhari a shafinsa na Tuwita, Shehu Sani, ya bukaci shugaba Buhari ya bude duk abinda aka bashi a rufe domin ganin mene ne a ciki.

DUBA WANNAN: Mamba a majalisar wakilai ya sha ruwan duwatsu a mahaifar sa

Cikin tsokana, Shehu Sani, ya ce "nan gaba ya kamata ka bude duk abinda aka baka a nannade domin ganin mene ne a ciki. Ko da babu wuta, to ka kunna fitila domin tabbatar da abinda ke kunshe cikin sakon. Farin dutse kanyi kama da zinare cikin duhun dare."

A satin da ya gabata ne wakilan kungiyar MLK suka kawowa shugaba Buhari ziyara a fadar gwamnatin tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel