Nigerian news All categories All tags
Harkar noma: Shinkafar gida na rage kudi a Gwamnatin Buhari

Harkar noma: Shinkafar gida na rage kudi a Gwamnatin Buhari

- Gwamnatin Shugaba Buhari ta nemi jama’a su komawa harkar noma

- Yanzu shinkafar my ta gida ta koma kusan N7500 a wasu kasuwannin

- Gwamnatin Buhari tayi alkawarin kudin shinkafa zai yi kasa da haka

Mun fahimci cewa kudin buhun shinkafa yana cigaba da yin kasa a Najeriya bayan da wani Bawan Allah ya shaida cewa ya ga canji da kan sa bayan da ya je kasuwa zai saye buhun shinkafar.

Harkar noma: Shinkafar gida na rage kudi a Najeriya

An fara sayen shinkafar gida a kan farashi mai sauki

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dage matuka a harkar noma kuma musamman na shinkafa inda hakan ya sa Najeriya ta rage shigo da shinkafa daga kasar waje domin a bunkasa harkar noman gida a kuma samu aikin yi.

KU KARANTA: Wani Bawan Allah ya sa kudi ga wanda ya kawo masa ayyukan Buhari

Wannan Bawan Allah mai suna Sadiq Omoola ya sanar da jama’a cewa shinkafar da ya saya N9000 a baya a kamfanin Olam ya ga irin ta ta koma N7500 a yanzu haka. Najeriya dai ta noma shinkafa sosai cikin ‘yan shekarun nan.

Dama dai Gwamnatin Shugaba Buhari tayi alkawarin cewa shinkafa za ta rage tsada da zarar an zage an yi noma. Idan aka samu yawan amfani, farashin kayan gona za su rage tsada domin a iya sayen na gida kuma yanzu an kama hanya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel