Nigerian news All categories All tags
Mamba a majalisar wakilai ya sha ruwan duwatsu a mahaifar sa

Mamba a majalisar wakilai ya sha ruwan duwatsu a mahaifar sa

Wasu fusatattun matasa sun yiwa dan majalisar wakilai, Garba Hamman Julde, ruwan duwatsu a jihar Taraba.

Honarabul Julde na wakiltar mazabun Bali/Gassol dake Jihar Taraba, a majalisar wakilai ta kasa.

Rahotanni sun bayyana cewar fusatattun matasan sun yiwa dan majalisar ruwan duwatsun ne a jiya yayin rabon babura 11 da mota daya da ya yi ga wakilan jam'iyyar APC a mazabu da shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Bali.

Wani ganau, Musa Sandire, ya ce matasan sun fara jifan dan majalisar ne bayan ya gama jawabinsa yana kokarin fara raba makullan baburan ga wakilan jam'iyyar.

Mamba a majalisar wakilai ya sha ruwan duwatsu a mahaifar sa

Honorabul Julde

Sandirde ya ce matasan sun jefi Julde ne saboda ya kauracewa zuwa mazabar sa tun bayan zabe.

"A take matasan suka fara yi masa ihun "bama so" bayan ya gama jawabinsa tare da jifansa da duwatsu har saida 'yan sandan dake wurin suka dauke shi daga wurin taron," inji Sandirde.

DUBA WANNAN: Ba A Taba Shugaban Nijeriyar Da Ya Kama Kafar Buhari a Yaki Da Cin Hanci Ba - Adeniran

Wani daga cikin shugabannin jam'iyyar APC, Ibrahim Daka, a mazabar dan majalisar ya bayyana mamakinsa bisa yadda dan majalisar ya manta da jama'ar sa tsawon shekaru biyu, sai yanzu da zabe ke karatowa sannan zai zo ya fara rabon mota da babura.

Kokarin jin ta bakin dan majalisa Julde ya ci tura saidai daya daga cikin masu taimaka masa, da bai yarda a ambaci sunansa ba, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga jaridar The Cable tare da bayyana cewar dan majalisar zai yi jawabi ga manema labarai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel