Nigerian news All categories All tags
Sanata ya fallasa asirin yadda Shi da PDP suke magudin zabe fiye da shekaru 20

Sanata ya fallasa asirin yadda Shi da PDP suke magudin zabe fiye da shekaru 20

Tsohon mataimakin shugaban dattijai, Ibrahim Mantu, ya tona asirin yadda Shi da PDP suke da hannu dumu-dumu a magudin zaben da yake faruwa a kasar nan.

Tsohon Sanata kuma tsohon dan kwamitin amintattu na Jam'iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan Talabijin da Channels TV suka yi da Shi, inda ya ce tabbas ya bayar da gudunmawa wajen magudin zabe da kuma siyen ma'aikatan zabe tare da baiwa jami'an tsaro na goro don toshe bakinsu har da ma ma'aikatan sauran Jam'iyyu domin Su kau da kansu duk don jam'iyyarsu ta PDP tayi nasara.

Yace: "Kwarai kuwa nayi, amma ga shi yanzu ina tona asirin abinda ya faru. Ba sai nayi magudin da hannu na ba, amma idan muka samar da kudi za suyi duk abinda mu ke da bukata. Kamar bawa ma'aikatan INEC kudi, su kuma da zarar sun samu wata dama, sai suyi kokarin yi mana abinda ya kamata. Jami'an tsaro ma haka mu ke basu, dukkan nin zabubbukan da suka gabata fiye da shekaru 20.

Ko da kuwa bana takara, amma in dai dan Jam'iyya ta yana yi, to lallai na fi so ya samu nasara. Yadda kuwa muka saba yi shi ne; da ma'aikatan zabe da Jami'an tsaro da sauran Jami'an ragowar jam'iyyun adawa, mu kan ware musu kasonsu don kar su bamu matsala. Ka ga kenan ko Ni da kaina ko kuma na bayar da wata gudunmawa wajen aikatawa, duk dai-dai yake da nayi magudi ko murde zabe."

KU KARANTA: Yan ta'adda sun hallaka Mutane a Borno bayan wani arangama da Sojoji

"Imani na shi ne, mutane irinmu da suka tuba, muna da masaniyar cewa har sai an samu mai bayarwa sannan za'a samu mai karba. To ya zama dole a mai bayarwa ya daina don mai karba kar ya ma gani balle ya sa rai" A cewarsa.

Wannan hira da aka yi dai ta janyo kace-nace a tsakanin al'umma, yayin da wasu suke ganin ya kamata tsami'an tsaro su damke Shi don ya fuskanci hakunci dai-dai da laifinsa.

Ibrahim Mantu ya kuma ce, "Na gaji da yadda ake min kallon mara gaskiya ko mai laifi a idon duniya, kawai don Ni dan Najeriya ne." kamata yayi a ce kowa bai da laifi har sai an tabbatar a gaban hukuma, amma da zarar ka bar Najeriya kallon mai laifi ake maka ko da kuwa Limami ne kai Pastor, kawai saboda ka fito daga Najeriya."

"Ina fatan wannan tonan sililin da nayi ya zama hanyar kawo gyara don na gaji da yadda nake ganin mutane cikin bakin talauci da kunci da kuma fatara. kullum sai wani yazo ya ce maka matarsa ta haihu ko dai wata matsalar ta daban, kaga idan da kowa na cikin wadata ai ba mai damun wani da roko.

Muna da arzikin da zamu iya yin rayuwa a wadace a cikin jin dadi a Najeriya ba tare da muna shan wahala ba, balle har a samu mabarata, amma rashin samun shugabanci na gari ne duk ya janyo mana halin kuncin da muke ciki. A saboda haka tilas mu samar da shugabannin da al'umma ce a gabansu ba sata ba da zasu gudanar da shugabanci da tafiyar da gwamanti ta kwarai sannan mu fita daga cikin halin da muke ciki. Ina mai tabbatar muku da cewa, irin wadannan Shugabannin Su ne mafitar mu."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel