Nigerian news All categories All tags
Dalilina na watsi da sunan sarautar Yoruba da rungumar na Hausa

Dalilina na watsi da sunan sarautar Yoruba da rungumar na Hausa

Wani sarki mai daraja ta daya a yankin kudu maso yamma na 'yan kabilar Yoruba, Abdulrasheed Akanbi, Oluwo na kasar Iwo, ya yi watsi da sunan sarautar sa na yaren Yoruba, "Oba", tare da rungumar sunan sarautar Hausa na "Sarki", domin a cewar sa, sunan yafi dadi da kyau.

Da yake kare matakin da ya dauka na rungumar sunan sarautar kabilar Hausa, Akanbi, ya ce rashin hadin kai tsakanin sarakunan kabilar Yoruba ya saka shi yanke shawarar daukar salon sarauta irinta sarakunan kasar Hausa.

A jiya Asabar ne Sarki Akanbi ya nada wani malamin addinin Islama, Yahqub Abdul-Baaqi Mohammed, a matsayin wazirin kasar Yoruba duk da adawar da kungiyar sarakunan yankin suka nuna a kan yunkurinsa na yin hakan.

Dalilina na watsi da sunan sarautar Yoruba da rungumar na Hausa

Sarkin kasar Owo ta kabilar Yoruba; Abdulrasheed Akanbi

Nadin sabon wazirin ya sha suka daga kungiyar masu rike da sarautar gargajiya a yankin kudu maso yamma da ma wasu yankuna na jihohin Delta da Edo dake yankin kudu maso kudu. Sarakunan sun bukaci sarki Akanbi ya yi nadin sarautar da suna masarautar sa amma ba da sunan yankin 'yan kabilar Yoruba ba.

Saidai a wata hira da ya yi da jaridar Premium Times a jiya ta wayar tarho, Sarki Akanbi, ya ce, kungiyar sarakunan gargajiya ta kabilar Yoruba ta dade tana fama da rigingimu, a saboda haka bai yi mamakin adawar da suka nuna da matakin da ya dauka ba.

DUBA WANNAN: Kaima fa ba wani mai tsarki bane - PDP ta bankado badakala a mulkin Buhari

"Zan kasance mai koyi da duk wani abu mai kyau. Babu hadin kai a tsakanin masu rike da sarautar gargajiya a yankin kabilar Yoruba, kullum cikin gulma da cin dunduniyar juna muke. Akwai cin hanci a tsakanin sarakunan mu. Nayi iya bakin kokarina wajen hada kanmu. Ina son al'ada ta da kishin kabila ta, saidai mun kasa hada kanmu," a cewar sarki Akanbi.

Sarki Akanbi ya kara da cewa, "Ka taba ganin sarakunan arewa na fada da junansu a bainar jama'a ko su dinga yin sharri ga junansu ta hanyar kiran wani daga cikinsu dan damfara? Akwai hadin kai tsakaninsu kuma hakan ya bani sha'awar canja sunan sarauta ta zuwa na Hausa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel