Nigerian news All categories All tags
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya kiristoci murnar bikin Easter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya kiristoci murnar bikin Easter

A jawabinsa na taya yan uwa mabiya addinin kirista bikin easter, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukace su da suyi amfani da wannan lokaci mai muhimmanci ta hanyar nuna kyawawan koyarwar addinin kirista, kamar nuna kauna ga makoci da sauran abokan zaman tare.

Ya yi kira gare Su da Su kauracewa Cin-hanci da rashawa da ta’addanci da kuma kalaman batanci da suke nuna kiyayya duk duk wani nau’i na abin da ke iya haddasa rigima a cikin al’aumma. Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune suka rawaito.

KU KARANTA: Ka bayyana yadda tiriliyan N1.1tn ta bace a mulkin ka - PDP ta kalubalenci Buhari

Rahotannanin da Legit.ng dai ta tattaara sun nuna cewa, Shugaban ya kuma yi kira da mabiya addinin na kirista da sauran jama’a da suyi amfani da wannan dama ta hanyar yin koyi da abubuwan alherin da ranar take nunawa.

“Soyayyar da zamu nuna wa juna da kuma kin karbar cin hanci da rashawa tare da yiwa juna uzuri da kauracewa kalaman kiyayya zasu taimaka matuka wajen gina kasarmu. Najeriya. Duk da kaluban da Kasar nan ke fuskanta, wannan lokaci ne na nuna kauna da tausayi da yafiya da kuma sa rai da rahamar Ubangiji." A cewar Shugaban Kasar.

Sannan ya kara da, “Samun dukiya ba shi ne ke nuna tabbacin samun farin ciki a rayuwa ba; amma soyayyarka da Ubangiji da sauran bayinsa ita ce mafi girma da cikar farin ciki”.

Shugaban ya kuma yi godiya da goyon bayan da ake wa gwamnatinsa da kuma kara tabbatar da yin kokari wajen tabbatar da samuwar aiki da cigaba da wanzuwar zaman lafiya tare da adalci. Kana kuma yayi gargadi ga yan siyasa masu haddasa husuma da furta kalaman batanci da na kiyayya da su farga su daina.

KU KARANTA: Masoya sun kashe Kansu a Ingila rungume da juna, inda suka shiga gaban Jirgin Kasa

Muhammadu Buhari ya sake nuna jin dadinsa da sakin yan Matan makarantar Dapchi da akayi tare da addu’ar sako ragowar na Chibok da ma sauran duk wadanda aka kame, sannan yace ya sanya a kuma tsaurara tsaro a sansanin yan gudun Hijira. Kuma ya sake ya jadda aniyarsa ta gudanar da sahihin zabe a 2019, wanda jama’a zasu zabin wanda suke so ta hanyar kada kuri’arsu.

Buhari ya ce, “bikin na Easter na bana ya sabunta fata da kwarin gwuiwar da muke da shi na ganin Najeriya ta gyaru”.

Legit.ng ta rawaito muku a baya cewa, Gwamnatin tarayya ta sanar da Juma’a 30 ga wata da kuma Litinin 2 ga wata matsayin ranakun hutu. A wata sanarwa da Ministan cikin gida janar Abdulrahman Dambazau mai ritaya ya bayar, a ranar Talata 27 ga watan Maris, ta hannun mai kula da aiyuka a ofishin Sakataren Gwamnatin tarayya Julie Ejiofor.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel