Nigerian news All categories All tags
Shugabancin jam'iyyar APC: Dakarun 'yan siyasa da kan iya maye gurbin Oyegun

Shugabancin jam'iyyar APC: Dakarun 'yan siyasa da kan iya maye gurbin Oyegun

- A ranar 26 ga watan Fabrairu ne kwamitin zartarwar jam'iyyar APC ya amince da karin wa'adi ga shugabannin jam'iyyar na kasa

- A satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya bayyana cewar karin wa'adin ya sabawa dimokradiyya da tsarin jam'iyyar APC

- Manyan 'ya'yan jam'iyyar APC sun fara kulle-kullen maye gurbin shugaban jam'iyyar, Oyegun, a zaben shugabannin jam'iyyar da za a yi 30 ga watan Yuni

A ranar 26 ga watan Fabrairu ne kwamitin zartarwar jam'iyyar APC ya amince da karin wa'adi ga shugabannin jam'iyyar na kasa.

Batun karin wa'adin ya jawo cece-kuce da fuskantar tirjiya daga wurin wasu 'ya'yan jam'iyyar. Kazalika, jam'iyyun adawa sun yi ca a kan jam'iyyar APC tare da bayyana cewar yin hakan ya sabawa dimokradiyya da kuma kundin tsarin mulkin jam'iyya.

A satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya bayyana rashin goyon bayansa ga tsarin tazarcen shugabannin jam'iyyar tare da bukatar APC ta gudanar da zaben sabbin shugabannin jam'iyya a ranar 30 ga watan Yuni, kamar yadda yake a tsarin mulkin jam'iyyar.

Shugabancin jam'iyyar APC: Dakarun 'yan siyasa da kan iya maye gurbin Oyegun

Shugaban jam'iyyar APC, Oyegun, da Buhari

A yayin da jam'iyyar ta bayyana aniyarta na barin kujerar shugabanta a yankin kudu maso kudu, hankula sun koma kan dakarun 'ya'yan jam'iyyar da kan iya maye gurbin shugaban jam'iyyar APC, Oyegun.

Adams Oshiomhole: Tsohon gwamnan jihar Edo, yana da goyon bayan shugaba Buhari da jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu.

A yayin wani taro a jihar Edo da aka yi a shekarar 2016, an rawaito shugaba Buhari na daukar alkawarin bawa Oshiomhole mukami a gwamnatin tarayya kafin karewar wa'adin mulkinsa.

DUBA WANNAN: Kurunkus: Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wadanda suka saci kudin gwamnati lokacin mulkin PDP

Dakta Ogbonnaya Onu: Tsohon shugaban tsohuwar jam'iyyar APP da ta rikide ta koma ANNP kafin daga bisani tayi maja da ragowar jam'iyyu su samar da APC.

Onu ya fito ne daga yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo kuma shine zababben gwamnan jihar Abiya na farko.

Onu, ministan kimiyya da fasaha a yanzu, dan siyasa ne mai ladabi da sanin makamar aiki.

Sanata Ken Nmani: Tsohon shugaban majalisar dattijai ta kasa lokacin zangon karshe na mulkin tsohon shugaban kasa Obasanjo, dattijo ne dake da kima da mutunci a yankin kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo.

Masu nazarin al'amuran siyasa na ganin cewar zaben Nmani a matsayin shugaban jam'iyyar APC zai kawo karshen baya-baya da 'yan kabilar Igbo keyi da jam'iyyar.

Saidai babban kalubale da Sanata Nnamani ke fuskanta shine, bai dade da canja sheka zuwa jam'iyyar APC ba daga tsohuwar jam'iyyar sa ta PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel