Yadda wasu 'yan Najeriya ke kasuwanci da fadan Boko Haram - Tsohon Gwamna

Yadda wasu 'yan Najeriya ke kasuwanci da fadan Boko Haram - Tsohon Gwamna

Tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas dake a kudu maso kudancin Najeriya na farko a wannan jamhuriyar, Mista Donald Duke a ranar Alhamis din da ta gabata ya yi ikirarin cewa asarar da Najeriya ta tafka sakamakon fadan Boko Haram ya fi wadda ta yi a lokacin yakin basasa.

Mista Duke dai ya yi wannan ikirarin ne a yayin zantawa da manema labarai a garin Legas, karkashin inuwar wata kungiya da ke rajin tabbatar da shugaba mai inganci a Najeriya watau National Movement for Positive Change (NMPC).

Yadda wasu 'yan Najeriya ke kasuwanci da fadan Boko Haram - Tsohon Gwamna

Yadda wasu 'yan Najeriya ke kasuwanci da fadan Boko Haram - Tsohon Gwamna

KU KARANTA: Buhari yayi wa TY Danjuma martani

Haka zalika tsohon gwamnan kuma ya kara fallasa cewa rikicin na Boko Haram ko shakka babu ya mayar da wasu hamshakan masu kudi inda suka mayar da abun tamkar wata sabuwar kasuwa da ta bude kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu.

A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan jihar Sokoto na farko a wannan jamhuriyar kuma jigo a jam'iyyar PDP a jihar yanzu haka watau Alhaji Attahiru Bafarawa ya yi ikirarin cewa tsaffin gwamnonin nan na jam'iyyar PDP da suka sauya sheka ya zuwa APC a shekarar 2014 sun baiwa sabuwar jam'iyyar ta su kudin kamfen na Naira miliyan 500.

A cewar sa, kafin jam'iyyar ta APC ta amince da dawowar su tare kuma da mallaka masu ragamar jam'iyyar jihohin nasu a hannun su sai da aka umurce su da kowa ya bayar da Naira miliyan 100.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel