Shugaban jam'iyyar APC: Mutane 3 da ake zaton za su maye gurbin Cif Oyegun

Shugaban jam'iyyar APC: Mutane 3 da ake zaton za su maye gurbin Cif Oyegun

Biyo bayan jawabin shugaba Muhammadu Buhari dake zaman babban jigo kuma shugaban jam'iyya mai mulki ta APC a matakin kasar a wajen taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar da kuma majilisar zartaswa, yanzu dai kusan a iya cewa wa'adin mulkin Cif Oyegun ya zo karshe a jam'iyyar.

To sai dai tuni har wasu sun fara nuna sha'awar su ta maye gurbin na Cif Oyegun idan lokacin zaben yayi wadanda kuma ake sa ran dukkan su za su fito daga yankin kudu ne.

Kawo yanzu dai ga wadanda aka fara rade-raden cewa su nuna sha'awar su ta jagorancin jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar APC: Mutane 3 da ake zaton za su maye gurbin Cif Oyegun

Shugaban jam'iyyar APC: Mutane 3 da ake zaton za su maye gurbin Cif Oyegun

KU KARANTA: Zamfara: Sarkin Anka ya nemin taimakon majalisar dinkin duniya

1. Adams Oshiomhole: Wannan dai tsohon fitaccen dan gwagwarmaya ne tun a lokacin kungiyar kwadago sannan kuma tsohon gwamnan jihar Edo ne.

2. Dakta Ogbonnaya Onu: Yanzu haka shine babban minista a ma'aikatar kimiyya da fasaha a Najeriya kuma dan kabilar Ibo ne daga shiyyar kudu maso gabashin kasar na.

3. Sanata Ken Nnamani: Shima dai dan kabilar Ibo ne kuma tsohon dan PDP ne da ma ya taba zama shugaban majalisar dattijai a shekarun baya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel