Bayan afkuwar hatsari, hukumar FRSC ta yi tsintuwar N2.09m

Bayan afkuwar hatsari, hukumar FRSC ta yi tsintuwar N2.09m

A wani mummunan hatsarin mota da ya afku, hukumar kula da manyan hanyoyi ta FRSC a reshen ta Legas da Ibadan, ta yi tsintuwar Naira 2, 096, 770, inda ta mayar da wannan dukiya zuwa ga 'yan uwan wanda ibtila'in ya afkawa a yau Asabar.

Hukumar yayin bayar da wannan tsintuwa ga macancanta

Hukumar yayin bayar da wannan tsintuwa ga macancanta

Hukumar ta yabawa jami'an ta na reshen Ogunmakin da wannan kyan kai da kyautatawa da ta yi na mayar da makudan dukiya ga 'yan uwan wanda hatsarin ya shafa bayan ta kammala bincike na tabbaci.

KARANTA KUMA: Badakalar Makamai: Jami'an 'yan sanda za su fara binciken gidaje a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar ta watsa jami'an ta sama da 300 da motocin sintiri 13 a birnin Minna na jihar Neja a sakamakon ziyarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dakarun soji sun katse hanzarin wasu 'yan tadda hudu a gabar Dajin Sambisa na birnin Maiduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel