'EFCC ta Kano' ta gano inda aka boye N100m da aka sace daga kudaden kananan hukumomi

'EFCC ta Kano' ta gano inda aka boye N100m da aka sace daga kudaden kananan hukumomi

- An sace kudaden ne daga asusun kananan hukumomi a Kano

- Hukumar hana cin hanci a Kano ta bincika ta gano kudin N100m a bankin Stanbic

- Za'a fadada bincike don jin suwa suka kwashe kudaden

'EFCC ta Kano' ta gano inda aka boye N100m da aka sace daga kudaden kananan hukumomi

'EFCC ta Kano' ta gano inda aka boye N100m da aka sace daga kudaden kananan hukumomi

Hukumar hana tu'annati da satar kudaden gwamnati ta jiha, watau Kano State Public Complaint and Anti-Corruption Commission, ta bankado wata babbar badakala wadda ta shafi tsohuwar Kwamishiniyar jihar da ta ajje aikinta a watan Fabrairu.

An gano wasu kudade ne da suka kai N100m na kananan hukumomi, wadanda aka kwashe daga asusun bai daya na kananan hukumomi, aka kuma mika su ga wani asusun tun a 2016 domin su haihu.

Wannan dai babban laifi ne da ya shafi kananan hukumomii da sauran dokoki da suka shafi bankuna da hada-hadar kudi da ma aikin gwamnati.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta nesanta kanta daga Wahabiyanci

Ashe wannan binciken da ma wasu dalilai na daga cikin dalilan da ya sanya Hajiya Aisha Mohammed Bello kwamishiniyar kudi ajiye aikinta.

Binciken ya nuna, ta hada kai ne da Managing Director ta Grassroots Micro Finance bank, Hajiya Farida M. Tahir inda aka ajje kudin, watakil kuma boyo ne, ko dai don riba, ko kuma don lamushe su in an manta dasu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel