Nigerian news All categories All tags
'Kamata yayi Najeriya ta halarta amfani da kwayoyi da basu da illa, kamar su wiwi'

'Kamata yayi Najeriya ta halarta amfani da kwayoyi da basu da illa, kamar su wiwi'

- Akwai kayan maye da basu da illa inji bincike

- Kurkukun Najeriya sun cika makil da jama'a

- Wasu suna ganin wiwi tana da alfanu

'Kamata yayi Najeriya ta halarta amfani da kwayoyi da basu da illa, kamar su wiwi'

'Kamata yayi Najeriya ta halarta amfani da kwayoyi da basu da illa, kamar su wiwi'

Tsohuwar Shugabar kasar Switzerland, Madam President Ruth Dierfuss, tace kamata yayi Najeriya ta halarta wasu daga cikin miyagun kwayoyin da aka haramta domin duniya tayi gaba ta bar Najeriya a gyaran dokoki, da ma binciken kimiyya.

Ta fadi hakan ne a zantawa da 'yan jaridar Premium Times, ya gefen taron duniya kan miyagun kwayoyi da kungiyar da take wa jagora a yanzu, ta yaki da muggan kwayoyi, Global Commission on Drug Policy wanda ake yi a babban birnin Tarayya, tace.

DUBA WANNAN: Miyagun kwayoyi Tramadol tafi kowacce illa

Wasu kasashen tuni sun baro wasu kwayoyin irinsu wiwi a matsayin kwaya, sun koma shanta a matsayin mmagani da likita zai rubuta maka.

A cewarta kuma, Afirka bata sayo kwayar Morphine, domin rage zafi da radadin ciwo, wanda hakan ke sanya wa mutane komawa wasu kwayoyin da ba aikinsu kenan ba. Inda tace gwamnatocin Nahiyar na tsoron ita ma morphine din, tunda tana da makalewa jini, zata iya zama sabuwar kwayar maye.

Ta kuma shawarci gwamnatocin yankin da cewa, dole ne su amshe cinikayyar muggan kwayoyi su hana masu hada-hadar kwayoyin samun kazamar riba da kudi, su kuma yi dokoki masu ma'ana, masu taiya da zamani, don kaucewa samuwar karfafan masu sana'ar masu in karfin gwamnati a nan gaba..

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel