Nigerian news All categories All tags
Dakarun Soji sun aikata 'yan ta'adda 4 na Boko Haram a gabar Dajin Sambisa yayin kunar bakin wake

Dakarun Soji sun aikata 'yan ta'adda 4 na Boko Haram a gabar Dajin Sambisa yayin kunar bakin wake

Rahotanni da sanadin jaridar Sahara Reporters wanda ta kalato daga shafin jaridar nan ta Punch sun bayyana cewa, a ranar yau ta Asabar ne dakarun soji suka katse hanzari wasu miyagun 'yan ta'adda 4 na Boko Haram a kauyen Malumti dake gabar Dajin Sambisa.

Mataimakin Kakakin rundunar Sojin dake gudanar da atisayen Zaman Lafiya Dole a garin Maiduguri, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.

Nwachukwu ya bayyana cewa, 'yan ta'addan hudu sun mutu murus yayin wani simame da dakarun Sojin suka kai musu bayan sun yi yunkurin tserewa atisayen dakaru a ranar 30 ga watan Maris.

Dakaru sun kashe 'yan ta'adda 4 na Boko Haram a Dajin Sambisa

Dakaru sun kashe 'yan ta'adda 4 na Boko Haram a Dajin Sambisa

Ya ci gaba da cewa, Dakarun sun yi nasarar damko wata mota kirar Toyota Land Cruiser baya ga muggan makamai na kare dangi a wajen 'yan ta'addan.

Kakakin sojin yake cewa, wannan 'yan ta'adda na kunar bakin wake da suka hadar da namiji guda da mata uku sun gamu da ajalin su a ranar Juma'ar da ta gabata, a yayin da suke neman hanya ta kurdawa cikin birnin Maiduguri domin aikata ta'asa.

KARANTA KUMA: Anyi cecekuce a zaman ganawa na shugabannin jam'iyyar APC

Rahotanni sun bayyana cewa, dakarun hadin gwiwa na farar hula sun taka rawar gani wajen dakile wannan 'yan ta'adda a kan hanyar su ta Muna Zawiya da misalin karfe 9.30 na dare.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta samu lambar ta fadar shugaban kasa sakamakon fice da tayi wajen inganta harkokin kasuwanci da habaka tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel