Nigerian news All categories All tags
2019: Ra'ayin Dattijan Yarabawa ya kasu kan burin Buhari a 2019 bayan ziyararsa ta makon nan

2019: Ra'ayin Dattijan Yarabawa ya kasu kan burin Buhari a 2019 bayan ziyararsa ta makon nan

- An kusa shiga zabukan 2019 a Najeriya, kuma ga dukkan alamu Buhari yana neman takara

- Yammacin Najeriya ne suka bashi babbar dama a 2015 karkashin Tinubu

- Yanzu kam sun ki bashi hadin kai 100/100

2019: Ra'ayin Dattijan Yarabawa ya kasu kan burin Buhari a 2019 bayan ziyararsa ta makon nan

2019: Ra'ayin Dattijan Yarabawa ya kasu kan burin Buhari a 2019 bayan ziyararsa ta makon nan

Tun bayan ziyararsa yankin na yammacin Najeriya, wanda mahanga ke ganin somin tabi ne na nuna alamar ana tare domin goyon bayyan tazarce a 2019, dattijan Yarabawa na yankin sun fara tofa albarkacin bakinsu kan ziyarar da ma makomar siyasar Buharin a yankin.

Wadanda suka zabta da 'yan jarida, wadanda sun hada da dattijon Afenifere, Chief Ayo Adebanjo, wanda ya kirkira Oodua Peoples Congress, OPC, Dr Fredrick Fasehun, Senator Femi Okurounmu, Chairman na hadakar shuwagabannin APC a jihohi da ma shugaban jam'iyyar APC a Lagos , Chief Henry Ajomale, sai kuma Pioneer President, Nigeria Labour Congress, NLC, Alhaji Hassan Summonu, watau uban tafiyar Kwadago ta NLC.

DUBA WANNAN: Martanin Shehu Sani kan batun bashin Kaduna a Majalisa

A yayin da wasunsu ke ganin ziyarar bata da wata ffa'ida banda sayen bakin yankin domin tazarce, wasuu kuwa gani suke ziyarar tayi armashi, kuma shugaban ya tabuka abin a yaba masa a tsawon mulkinsa.

A ziyarar dai, banda ayyukan jiha da ya kaddamar babau wani aikin gwamnatin Tarayya da ya bude ko aka yi bikin dora damba, wanda alama ce da ke nuna akwai wadanda zasu ce babu alfanu a zaben da suka yi masa a 2015.

Daga cikin dattijan da suka tauna, Ayo Adebanjo, yace ziyarar, bata da wani alfanu banda bata lokaci da yawon bambadanci bayan ga inda ya kamata shugaban ya ziyarta. "Kashe-kashen Makiyaya da ma sace mutane yayi kamari a kasar nan, can ya kamata shugaban yaje ba bikin taya Tinumbu murna ba.

Shi kuwa Fasehun cewa yayi, ziyarar bayan cewa ba'a makara ba, tana da muhimmanci, kuma ta ma yi armashi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel