Nigerian news All categories All tags
An rasa rayuka 5, wasu 13 sun jikkata a wani sabon harin bam da aka kai Maiduguri

An rasa rayuka 5, wasu 13 sun jikkata a wani sabon harin bam da aka kai Maiduguri

A kalla mutane biyar sun riga mu gidan gaskiya kuma wasu mutane 13 sun sami munanan raunuka ciki har da wani Farfesa sakamakon wata sabon harin bam da aka jai a garin Maiduguri kamar yadda mazauna garin da 'yan civilian JTF suka tabbatar.

Yan kunan bakin waken da ake kyautata zaton yan kungiyar Boko Haram ne sun isa garin Muna Zauyar da ke karamar hukumar Mafa da ke Maiduguri misalin karfe 8.45 na dare inda sukayi sanadiyar mutuwar wata mace, akuyoyi hudu, kare guda daya da kuma raunana al'umma da dama.

Mutum 5 sun mutu, wasu 13 sun jikkata a wani harin bam da aka kai a Maiduguri

Mutum 5 sun mutu, wasu 13 sun jikkata a wani harin bam da aka kai a Maiduguri

"Wata mace ta mutu kuma wasu mutane 13 sun jikkata ciki har da Farfesa Khursa Imma na sashin nazirin shari'ar addinin muslunci da ke Jami'ar Maiduguri wanda ya sami rauni tare da yayan sa guda biyu wanda a halin yanzu suna karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri" kamar yadda jami'in CJTF ya sanar da jaridar Daily Trust.

KU KARANTA: Zaben 2019: Kuyi takatsantsan da gwamnatin Buhari - Sakon kungiyar Obasanjo ga 'yan Najeriya

Mai magana da yawun hukumar Yan sanda na jihar Borno, DSP Edet Okon ya tabbatar da faruwar harin a wata sanarwa da ya aike ga manema labarai a safiyar yau.

A cikin sakon ya tabbatar da cewa a jiya misalain karfe 9.49 na dare 'yan kuna bakin wake (mata) guda 4 sun sami shiga garin Muna Zawuya da ke karamar hukumar Mafa a wajen garin Maiduguri. Sun kuma tayar da bam wanda yayi sanadiyar mutuwar su tare da wata mace guda daya tare da raunana mutane 13.

Rundunar Yan sandan ta aike da jami'anta don gudanar da bincike a wurin da abin da ya faru tare da kara tsaurara matakan tsaro don tabbatar da cewa al'umma sunyi shagulgulan Easter cikin lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel